1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Arusha don sasanta yan tawayen Dafur

August 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuEt

A yau a birnin Arusha na ƙasar Tanzania ake fara taron kwanaki uku ta samar da daidaito da fahimtar juna a tsakanin bangarorin yan tawayen Dafur bayan amincewa da gagarumin shirin rundunar haɗin gwiwa na Majalisar ɗinkin duniya dana Afrika domin aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur. Taron wanda ƙungiyar gamaiyar Afrika da Majalisar ɗinkin duniya suka ɗauki nauyin gudanar da shi zai fayyace matsayi na bai ɗaya da dukkan yan tawayen suka amince da shi domin fara wasu shawarwarin sulhun da gwamnatin Sudan. Tun da farko dai a lokacin ɓarkewar rikicin na yammacin Sudan kimanin shekaru da rabi da suka wuce ƙungiya guda ce ta yan tawayen ta ƙalubalanci gwamnatin ta Kahartoum, amma yanzu jakadu na fama da gumin goshi domin samun masalaha a tsakanin ƙungiyoyi daban daban na yan tawayen inda wasu ma ke ƙauracewa zaman shawarwarin. A halin da ake ciki babbar ƙungiyar yan tawayen SLM ta Abdulwahid Mohammed Nur tace ba zata halarci taron na Arusha ba saboda abin da ta baiyana da cewa rashin halascin wasu ƙungiyoyin yan tawayen da kuma sharaɗin samun tsagaita wuta mai ɗorewa kafin fara dukkan wata tattaunawa.