1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron APF a Libreville

July 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuGw

Majalisar dokokin ƙasashe masu anfani da halshen parasanci, ta buɗa zaman taron ta, a birnin Librevile na ƙasar Gabon.

A tsawan yini 2, yan majalisu fiye da 250, daga ƙasashe 40 na dunia, za su mahaurori a game da batutuwa daban-daban, wanda su ka haɗa da matsalolin baƙin haure, da kuma tashe tashen hankula da ke wakana a wasu ƙasashe membobin ƙungiyar, kamar su Libanon, Guinee, Tchad, da Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Kazalika, mahalarta wannan taro karo na 33, za su tantananawa, a game da yiwuwar sake karɓar Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo da Mauritania, a matsayin membobi, bayan zaɓɓuɓukan demokraɗiya da a ka shirya a wannan ƙasashe 2.

Shugaban ƙungiyar ƙasashe masu anfani da halshen paransanci Abdu Diouf, zai shi anfani da wannan dama domin gabatar da sakamakon ayyukan da ya ƙaddamar.