Taron Aids A Nigeria | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Aids A Nigeria

A birni Abuja na Tarayya Nigeria a na ci gaba da zaman taron kasa da kasa a game da cutar Aids.

Mutane a kalla 2000 daga sassa daban daban na Afrika ,da ma dunia su ka halarci bikin bude taron a jiya.

A tsawon kwanaki 6 za su masanyar ra´ayoyi a game matakan yaki da wannan cuta da kuma tabatar da haske da adalci acikin magudan kudaden da a ke sakawa, domin yaki da cutar Sida.

Sannan kurrarunn masana ta wannan fanni da kungiyoyin kasa da kasa za su mahaurori a kan hanyoyin yaduwar cutar da matakan riga kafi.

Nahiyar Afrika, fiye da sauran yankunan na dunia, na fama da cutar Aids ,inda kussan kashi 2 bisa 3, na jimmilar mutane million 40, da ke dauke da kwayoyin cutar ke raye a Afrika, mussaman ta kudu ga Sahara.