1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron addinin Musulunci a Jamus

An fara zagaye na biyu na babban taron addinin Musulunci a Jamus

default

Masaniyar kimiyyar addinin Musulunci Tuba Isik-Yigit (a hagu) da ministar iyali ta tarayya Kristina Schröder suna zantawa a lokacin babban taron addinin Musulunci a Berlin

A wannan Litinin a birnin Berlin aka buɗe zaman babban taro kan addinin Musulunci da gwamnatin Jamus ke ɗaukar nauyin gudanarwa. To sai dai manyan ƙungiyoyin Musulmai a ƙasar ta Jamus sun ƙauracewa taron, ɗaya bisa rashin amincewa da ajanda da kuma mahalarta taron sannan ɗayar kuma saboda zarginta da ake yi da almundahana da tallafawa reshenta da ake zargi da yaɗa tsattauran ra'ayi. Taron na tattaunawa ne kan wani tsarin koyar da addinin Musulunci ga Musulmai a Jamus. Hakazalika za a kuma tattauna game da ƙyamar da ake nunawa Musulunci da rawar da maza da mata ke takawa a cikin wannan addini. A shekara ta 2006 aka ƙirƙiro da taron da nufin kyautata shigar da Musulmai a harkokin yau da kullum a Jamus. Musulmai kimanin miliyan huɗu ɗaukacinsu 'yan asalin Turkiya suke a wannan ƙasa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas