Taron ƙungiyar yan jarida ta dunia a birnin Moscou | Labarai | DW | 06.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙungiyar yan jarida ta dunia a birnin Moscou

Ƙungiyar jaridu da mujjalu ta dunia, na ci gaba da gudanar da zaman taro a birnin Mosko, na ƙasar Rasha.

A ƙalla shugabanin kampanonin sadarwa dubu 17 ne, daga ƙasashe 110 na dunia, ke halartar wannan taro ,domin bitar matsaloli, da kuma nasarorin da aka samu, a wannan aiki.

A shekara bana, Ƙungiyar ta yan jarida, ta yanke shawara bada lambar yabo ta mussaman, ga Akbar Ganji, wani ɗan jarida, na ƙasar Iran da ya yi suna, ta fannin tsage gaskiya.

A sakamakon hakan hukumominTeheran, su ka kulle shi, a tsawan shekaru 6 kurkuku.

Akbar Ganji, ya fito daga gidan yari, a watan Maris da ya gabata.

A cikin jawabin da yayi, bayan samun kauttar, ya tabbatar da cewa, babu gudu, babu ja da baya, a game da binciko maganar gaskiya, da kuma bayanawa jama´a.

A nasa jawabi, shugaban ƙungiyar AJM, ya ƙalubalanci hukumomin Rasha, da take haƙƙoƙin yan jarida.………………………………………………