Taron ƙungiyar Asean a birnin Kuala-Lampur na Malaisia | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙungiyar Asean a birnin Kuala-Lampur na Malaisia

Ministocin harakokin wajen ƙasashen yankin kudu maso gabas na Asia sun buda zaman taron shekara shekara a birnin Kuala Lampur na ƙasar Malaisia.

Taron na gudana bisa gayyatar ƙungiyar Asean, da ta haɗa ƙasashe 10 na wannan yanki.

Mahimman batutuwan da za su tantanawa, sun shafi haƙƙoƙin bani adama,a Birmania, da rikicin makaman nukleyar Korea ta Arewa, da kuma halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Taron na shekara bana, zai samu halartar sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice.

Condee zata anfani da wannan dama,domin masanyar ra´ayoyi da ƙungiyar Asean, a game da batun makamai masu lizzami da Corea ta Arewa ta harba, kawanakin baya, da kuma nacewar da hukumomin Pyong Yang su ka yi, na ci gaba da, ta ƙera makaman nukleya, duk da kiranye kiranyen da dunia ke masu, na su ci tuwa fashi.

A dangane da rikicin Isra´ila da Hezbolah, a sanarwar share fage da su ka hido jiya, ministocin kungiyar Asean, sun bayan adamuwa, a game da halin da ake ciki, sannan sun bukaci ɓangarorin 2, su tsagaita wuta cikin gaggawa.