Taron ƙolin NATO a Lisbon | Siyasa | DW | 19.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙolin NATO a Lisbon

Taron na mayar da hankali kan sabbin dubaru ga ƙungiyar da za su dace da sabon fasalin duniya

default

Sakatare Janar na NATO Anders Fogh Rasmussen a taron manema labaru a birnin Lisbon gabanin buɗe taron ƙolin NATO

Ƙasashen ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO sun jima suna tattaunawa game da sabbin dubarun. To amma tambaya ita ce me ya sa NATO ke bukatar wata sabuwar alƙibla? Tun a shekarar 1999 aka kawo ƙarshen yaƙin cacar baka, kuma a wancan lokaci ne kuwa ƙungiyar ta amince da dubarun da take amfani da su kawo yanzu. To sai dai tun daga lokacin, siyasar duniya ta sauya a saboda haka ana bukatar sabbin dubaru da za su dace da zamanin nan da muke ciki.

Masu iya magana dai kan ce wai in kiɗa ya canza dole ma rawa ta canza. Tun a shekarar 1999 ƙungiyar tsaro ta NATO ta gudanar da irin wannan taron ƙoli kan dubarunta, biyo bayan faɗuwar katangar Berlin wato ƙarshen yaƙin cacar baka a duniya. To sai dai tun bayan wannan lokaci abubuwa da dama sun faru alal misali hare-haren 11 ga watan Satumban shekarar 2001, barazana daga 'yan tarzoma waɗanda tushensu ke a ƙasashe kamar Afganistan, ga kuma ci-gaban hanyar sadarwa ta Intanet wadda ke haɗa ba wai ƙawaye kaɗai ba a'a har ma da abokan gaba. Wato kenan ya zama dole NATO ta yi ta tafiya da zamani a fagen siyasar duniya. Roland Freundenstein masanin batutuwan tsaro ne a cibiyar nazarin harkokin nahiyar Turai dake birnin Brussels ya yi nuni da cewa har yanzu NATO ta ɗaura ɗamarar yaƙi ne irin na kare kai daga harin da za a kai yankunanta. Ya ce maimakon makamai da tsoffin dubaru da akwai buƙatar sabbin dubarun yaƙi.

"Ana buƙatar sabuwar alƙibla domin tinkarar ƙalubale na zamani. Za a iya sabunta dubbarun yaƙi ta hanyar amfani da makamai na zamani domin cimma burin da aka sanya a gaba."

NATO ta ƙuduri aniyar ƙarfafa haɗin kai da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai domin magance aukuwar rikice rikice ko kuma ɗaukar sahihan matakan magance su. Hakazalika za ta ƙarfafa dangantakar tsaro da Rasha dake zama tsohuwar abokiyar gabarta a lokacin yaƙin cacar baka, musamman wajen yaƙi da 'yan fashin jiragen ruwa da daƙile yaɗuwar makaman ƙare dangi.

To sai dai ba rundunar sojoji da dubaraun yaƙin kaɗai ke buƙatar gyaran fuska ba, wani ɓangare ne na sabbbin dubarun shi ne gina wani tsarin kariya daga harin rokoki. A taron baya-bayan nan na ministocin tsaro da na harkokin wajen ƙasashen NATO babban sakataren ƙungiyar Anders Fogh Rasmussen ya yi kira da ka da a bari shirin girke makaman kariya ya ruguje. To sai dai kuma batun kuɗi da kuma shawo kan Rasha ta ba da haɗin kai kan wannan tsari na daga cikin abubuwan da ake taƙaddama kansu. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle na mai ra'ayi da a haɗa batun kandagarkin harin rokoki da kwance ɗamarar makaman nukiliya.

"Muna da kyakkyawan fatan cewa sanarwar bayan taron na birnin Lisbon za ta yi taɓo irin rawar da rage yawan makaman nukiliya zai taka. Kuma za mu ba da ta mu gudunmawa, kana NATO za ta ba da tata gudunmawa wajen samun yarda juna da sa ido kan rage makaman ba tare da yiwa matakan kariya cikas ba."

Duk da sabbin dubarun da shugabannin na NATO suka ƙuduri aniyar samarwa, muhimmin batu ga ƙungiyar har yanzu shi ne alhakin da ya rataya kan kowace memba ta NATO wato kare juna kamar yadda aka saba tun shekaru 60 da suka wuce.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu