1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙolin MƊD da AU

An shirya taron tsakanin Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar AU don ƙarfafa haɗin kai tsakanin su

default

Ban Ki Moon

Babban sakataren Majalisar ɗinkin duniya Ban Ki Moon da Firaministan Birtaniya Gordon Brown da kuma shugabannin ƙungiyar tarayyar Afirka sun yi kira ga Zimbabwe da ta tabbatar da cewa sakamakon zaɓen shugaban ƙasar ya dace da abin da´al´umar ƙasar suke so kuma ka da a yi maguɗin sa. An yi wannan kira ne a taron haɗin guiwa tsakanin majalisar da kuma ƙungiyar AU a birnin New York.

To sai dai ɗaukacin mahalarta babban taron da ya ƙunshi manya jami´ai na kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya akan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro a Afirka sun yi watsi da halin da ake ciki a Zimbabwe bayan zaɓen da ya gudana a wannan ƙasa. Gwamnatocin yamma da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon sun yi gargaɗin cewa mutuncin Afirka zai zube a idanun duniya idan ba a samu sahihiyar demoƙuraɗiyya a wannan nahiya ba musamman a Zimbabwe. Mista Ban ya nuna damuwa game da halin da ake ciki a Zimbabwe yana mai cewa.

Ban "Na damu matuƙa game da halin rashin sanin tabbas da rashin bayyana sakamakon zaɓen a Zimbabwe ya haddasa. Duk wani jinkiri da za a ƙara samu kan wannan batu zai dagula al´amura ne wanda zai yi mummunan tasiri ga al´umar Zimbabwe."

Firaministan Birtaniya Gordon Brown wanda ƙasarsa ta taɓa yiwa Zimabwe mulkin mallaka, kashedi yayi cewa bai kamata duniya ta kyale shugaba Robert Mugabe ya sata ƙuri´un zaɓen shugaban ƙasar ba.

Firmaninista Brown ya ce: "Duk wanda ya ga yadda zaɓen ya gudana ya san cewa shugaba Mugabe bai yi nasara ba. Duk zaɓen da aka yi murɗiyarsa ba zai zama zaɓe na demoƙurɗiyya ba. Saƙon mu daga New York shi ne zamu ci-gaba da kare dokokin demoƙuraɗiyya muna bayan al´umar Zimbabwe masu muradin girke sahihiyar demoƙuraɗiyya, zamu ci-gaba da goya musu baya."

Shubaga Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu wanda ya ƙi fitowa fili ya soki lamirin Mugabe, yanzu ya na shan suka daga sauran manyan ƙasashen duniya.

An dai kiran taron kwamitin sulhun ne don tattauna hanyoyin ƙarfafa ayyukan kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar AU, wanda shugaba Mbeki ya ce yana fuskantar koma baya saboda rashin isassun kuɗi da kayan aiki.

Rikice rikice a nahiyar Afirka sun ɗauki kimanin kashi 60 cikin 100 na ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya. Yanzu dai an fara girke dakarun hadin guiwa tsakanin MDD da kungiyar AU a Sudan wanda idan an kammala shi zai ƙunshi sojoji dubu 30.