Taron ƙolin ƙungiyar APEC ya amince da yarjejeniyar kare muhalli | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙolin ƙungiyar APEC ya amince da yarjejeniyar kare muhalli

Shugabanni 21 na gamaiyar tattalin arzikin kasashen Asiya da Pacifik wato APEC a takaice sun sanya hanu kan wata yarjejeniya da nufin rage dumamar yanayia gun taron kolin su a birnin Sydney na kasar Australiya. Yarjejeniyar wadda bai wajaba a yi aiki da ita ba, ta yi kira da a dauki mataki na dogon lokaci da zumar rage fid da hayakin ne mai dumama doron kasa. Mai masaukin baki kuma FM Australiya John Howard ya ce yarjejeniyar wata shaida ce ga muhimmancin da kungiyar ke bawa yaki da dumamar doron kasa sannan a lokaci daya ta ke bin nagartattun hanyoyin bunkasa tattalin arziki.

Howard:

“An amince da yarjejeniyar birnin Sydney. A dangane da haka ina godewa dukkan shugabannin kungiyar APEC. Yarjejeniyar wani muhimmin mataki na amincewa da wani shirin kasashen duniya na kare muhalli. Tana bawa ko wace kasa damar daukar matakai da suka dace don tinkarar matsalar sauyin yanayi.”