1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙolin ƙarshen shekara na EU a Brussels

Shugabannin ƙasashen kungiyar tarayyar Turai EU sun fara gudanar da taron kolin su na karshen shekara a birnin Brussels. Muhimman batutuwan da taron ke mayar da hankali kan su sun hada da batun makomar lardin Kosovo. Ya zuwa yanzu kawunan membobin ƙungiyar ta EU sun rarrabu kan irin martanin da zasu mayar idan Albaniyawan Kosovo suka yi shailar samun ´yancin kai daga tarayyar Sabiya. Wasu ƙasashe na ƙungiyar na nuna adawa da amincewa da ´yancin kan Kosovo ba tare da wani ƙudurin MƊD da ya amince da wannan ´yanci ba.