1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙoli a kan cutar AIDS a birnin Toronto na ƙasar Canada

A ƙalla masana dubu 20 ne ta fannin kiwon,lahia su ka shirya zaman taron bita a kan cutar SIDA albarkacin cikwan shekaru 25 da ɓulluwar wannan annoba.

Traon wanda shine irin sa na 16 na wakana a birninToranto na kasar Canada.

Massanan, za su yi masanyar ra´ayoyi a kan halin da ake ciki a dangane da yaƙi da cutar AIDS.

A jimilce, sun nunar da cewa, an samu babban ci gaba, ta hanyar samar da maganin warkar da cutar, to saidai cigaban, ya banbanta daga wannan kasa zuwa wacen.

Bincikenda su ka guganar ya nunar da cewa a shekara da ta gabata mutane milion4 su ka kamu da cutar, kuma wannan addadi ya ja baya idan aka kwattanta, da yawan wanda ke kamuwa da ita, a shekarun da su ka gabata.

Ƙasashen da su ka fi fama da cutar, a halin yanzu, sun haɗa da India da kuma nahiyar Afrika.

Ƙasar Senegal ta samu kyaukyawan yabo, akan ƙoƙarin da ta nuna, wajen kokwa da cutar ƙanjamau, ta fannin faɗakar da al´umma, akan illolin ta, da kuma samar da maganin rage raɗɗaɗin cutar, ga wanda su ka kamu.