Taron ƙli na shugabanin EU | Siyasa | DW | 12.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙli na shugabanin EU

Shuagbanin ƙungiyar Tarayya Turai na tattanawa a game da ɗumamar yanayi,tattalin arziki da kundin tsarin mulkin EU

default

Taron ƙarshen shekara na EU a Brussels

Shugabanin ƙasashe ko na gwamnatocin Ƙungiyar Tarayya Turai sun shiga kwana na biyu kuma na ƙarshe a taronsu na ƙarshen shekara.

A yau sun maida hankali ne a game da batun ɗumamar yanayi.

Jine shugabanin EU suka buɗa wannan taro bisa jagorancin shugaban France Nikolas Sarkozy, shugaban karɓa karɓa na EU dake shirin barin gado.

Mahimman batutuwa guda ukku,  suka mamaye ajendar taro, wato ɗumamar yanayi,kudin tasrin mulkin EU, da kuma hanyoyin fita daga matsalar tattalin arzikin da ƙasashen duniya ke fama da ita.

Shugabanin sun fara mahaura a game da batun kundin tsarin mulki Tarayya Turai, wanda  a watan Juli da ya gabata,al´ummar ƙasar Irland tayi watsi da shi.

A sakamakon masanyar ra´ayoyin da suka yi, Irland za ta sake shirya zaɓe a game da wannan kundi, wanda cilas sai ya samu tabarakin dukan ƙasashe 27 na EU kamin ya fara aiki.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana shawar samun cimma daidato a game da wannan daftari.Tace:

Jamus ko shakka babu, na da muradin ganin an ƙaddamar da yarjejeniyar Lisbon da ta shinfiɗa kudin tsarin mulkin Ƙungiyar Tarayya Turai.

Yarjejeniyar Lisbon ta tanadi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin EU, ta yadda daga shekara ta 2014, za a daina tsarin shugabanin karɓa karɓa tsakanin ƙasashen EU.

Bayan batun kundin, magabatanTarayya Turai, a jiya sun cimma yarjejeniya  a game da hanyoyin warware matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da ta shafi kasashensu.

Saboda haka, sun ware tsabar kuɗi wuri na gugar wuri, har Euro Miliyan dubu 200, don taka birki ga wannan mummunar kariyar arziki wadda itace, irinta ta fako tun bayan yaƙin duniya.

Wannan kuɗi ya kai addadin kashi 1,5 cikin 100 na albarkatun cikin gida da ƙasashen suka mallaka a shekara.

A cewar Firaministan Luxemburg Jean Claude Junker, irin matakin da EU ta ɗauka domin magance matsalar hada -hadar kuɗi ,ya zama wajibi ta ɗauki wani makamancinsa, domin magance dumamar mahalli, ya kuma bada hujjoji kamar haka:Matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki mai wucewa ce,  a yayin da ta ɗumamar yanayi matsala ce ta dindindin, muddun ba a tanadar mata matakai ƙwaƙƙwara ba.

Saidai akwai saɓanin ra´ayi, a game da matakan bai ɗaya na magance wannan matsala tsakanin ƙasashen Ƙunghiyar Tarayya Turai, amma  shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta kyauata zaton za a samu fahintar juna:A ganina akwai kyakkyawar aniya tare da dukkan shugabanin , kuma nayi imani idan muka cigaba da tattanawa zamu cimma nasara kaiwa ga matakin bai ɗaya.

Cemma  a lokacin da yayi jawabin buɗe taron shugaban Ƙungiyar Tarayya Turai Nikolas sarkozy,yayi kira ga magabatan EU su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya a dangane da batun hanyoyin yaƙi da ɗumamar yanayi.