Taron ƙasashen ´yan ba ruwan mu | Labarai | DW | 13.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙasashen ´yan ba ruwan mu

Wakilai daga ƙasashe masu tasowa fiye da ɗari daya waɗanda ke halartar taro a birnin Havana na ƙasar Cuba, sun bada shawarar tattaunawa ba tare da sharuda ba domin sulhunta taƙaddamar nukiliyar Iran. Wakilai dake halartar taron na kwanaki shida sun yi kakkausar suka ga Israila sai dai kuma sun janye buƙatar yi mata hukunci a game da laifukan yaƙi. Yayin da jadawalin taro ya maida hankali a kan yankin gabas ta tsakiya inda ake sa ran halartar shugabanin ƙasashen Syria da Lebanon, a waje guda kuma ƙasar Venezuela na amfani da taron wajen neman goyon baya na samun wakilci a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya.

Babu tabbas ko shugaban ƙasar Cuba fidel Castro mai shekaru 80 da haihuwa zai halarci taron a karon farko tun bayan da ya kwanta rashin lafiya. Ana sa ran halartar shugabanin ƙasashe 50 ciki har da sakataren Majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan da shugaban ƙungiyar ƙasashen larabawa Amr Moussa da kuma shugaban hukumar ƙungiyar gamaiyar Afrika Alfa Omar Konare.