Taron ƙasashen musulmi na dunia a Indonesia | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙasashen musulmi na dunia a Indonesia

Yau ne a Indonesia , ƙasa mafi yawan musulmi a dunia, a ka buɗa wani zaman taro, da ya haɗa wakilai daga ƙasashen musulmi daban-daban na dunia.

Mahalarta wannan taro, za su masanyar ra´ayoyi, a game da hanyoyin ƙara haskaka tarmamuwar musulunci, da kuma shinfiɗa hanyoyin da, wanda ke da jahilci a game da wannan addini, za su fahintar sa.

A cikin jawabin da yayi, shugaban ƙasar Indonesia, Susilo Bambang Yudhoyono, yayi kira ga ɗaukacin musulmi da su buda kofofin su ga al´ummoin dunia, su kuma taimaka a magance da matsalolin da duniyar ke fama da su.

A nasa ɓangaren Praministan Malaisia, Abdullah Ahmad Badawi, ya yi suka ga kallon da kafofin sadarwa na turai da Amurika, ke wa musulunci, a matsayin wani addini, mai dangantaka, da ta´adanci.

Praministan ya bukaci ƙasashen musulmi na dunia, su bada himma, wajen batun illimi da tarbiya ga matasa, wanda,ta haka ne kawai ,a cewar sa,za a dassa aya ,ga masu ɓata sunann musulunci, ta hanyar kai hare haren ta´adanci.