Taron ƙasa na Jami′iyar kare muhalli a Jamus | Labarai | DW | 20.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ƙasa na Jami'iyar kare muhalli a Jamus

Greens ta amince da samar da makamashi mai daɗaɗawa muhalli

default

Wakilan jami'iyyar kare muhalli ta "The Greens" da ke nan Jamus, sun amince da amfani albarkatun da basu da illa ga muhalli wajen samar da makamashi cikin shekaru 20 masu gabatowa. Wakilan jam'iyyar da ke gudanar da taro a birnin Freiburg, kazalika sun kaɗa ƙuri'un amincewa da rage yawan iskar da masana'antu ke fitarwa da wajen kashi 95 daga cikin 100, nan da shekara ta 2050, tare da rufe cibiyar makamashin nukiliya na Jamus cikin gaggawa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Yahouza Sadissou Madobi