1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙasa da ƙasa a game da ruwa

Wakilai daga ƙasashen dunia na mahaurori a game da ruwa a Mexico

default

Wakilai daga Ƙasashen dunia, da ƙungiyoyin, daban-daban, na ci gaba da tabka mahaurori a Mexico, a game da ruwa, abukan aiki inji bahaushe.

Wannan babban taron ƙasa da ƙasa, wanda shine 4 irin sa, na ɗauke da burin binciko hanyoyin samar da tsabtatun ruwan sha, ga al ´ummomi, kimamnin million ɗari 5, a dunia, kamin shekara ta 2010.

Hukumar ruwa ta dunia, da ta kiri taron, ta bayyana cewar, a halin da ake ciki, mutane fiye da million dubu 1, ke anfani da gurbabatun ruwa sha, a dunia, sannan kussan million dubu 2, ba su da issasun matatun ruwa.

Wani bincike da hukumar kiwon lahia ta Majalisar Ɗinkin Dunia ta gudanar, ya gano cewa, a shekara ta 2004, cuttutuka, masu allaƙa da rashin tsabtattun ruwan sha ,sun yi sanadiyar mutuwar mutane kussan dubu 4, a ko wace rana.

A jawabai daban daban da wakilan hukumar ruwa, su ka gabatar a wannan taro, sun nunar da cewa, akwai albarkatun ruwa masu yawa, a ƙarkashi, da kuma a bilbishin ƙasa, to saidai magabatan ƙasashe, mussaman masu tasowa, basu ɗauki inganttattun mattakai ba, na sarrapa wannan arziki don wadata jama´ar su, ta ruwa tsabtattu.

A nata ɓangare, majalisar Ɗinkin Dunia ta nunar da cewa, a na assara ta a ƙalla kashi 40 bisa 100, na tsabttattun ruwan da ake tacewa, ta hanyar rashin ingancin makwararan rarraba su, da kuma jonin ruwa na bayan fage, da wasu ke yi a gidajen su, ba tare da sanar da hukumomin da, yaunin aikin ya rataya a kan su ba.

A lokacin da aka girka hukumar dunia mai kullka da ruwa, ƙasashe da dama, sun kauttata zaton , ba tare da ɓata lokaci ba, zata taimaka wajen magance matsalolin ruwa a ƙasashe masu tasowa.

To amma shekaru 10 da girka ƙungiyar har yanzu, da sauran rina kaba.

Albarakacin buɗa taron na Mexico, dubunan mutane su ka shirya zanga zangar yin Allah wadai da shi.

A nasu tunani wannan taro da a ke kira ko shekara 3 zuwa shekara 3, bai da wani tasiri ta fannin magance matsalar ruwa.

Maimakon hakan, ƙasashe masu hannu da shuni, da kampanoni masu zaman kann su da aiki ta fannin ruwa na amfani, da wannan dama, domin ƙara ɓullo da hanyoyin cushe mattakan samar da ruwa ga tallakawa.

Shugaban hukumar ruwa ta dunia, Loic Fauchon, ya yi kira ga ƙasashe masu arzikin massana´antu, da ƙungiyin bada agaji, da su ƙara yawan tallafin da su sakawa wajen al´ammuran samar da ruwa.

A halin yanzu, inji wannan jami´i kashi 5 kaɗai bisa 100, na taimako a faɗin dunia, ke nufa ta hanyar ruwa, alhalin su ne tushen rayuwa
 • Kwanan wata 17.03.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu17
 • Kwanan wata 17.03.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu17