Taron ƙasa da ƙasa a game da Afganistan | Siyasa | DW | 31.03.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙasa da ƙasa a game da Afganistan

Ƙasashen duniya sun himmantu domin samar da zaman lafiya a ƙasar Afganistan

default

Taron cimma zaman lafiya a Afganistan

Yau ne a birnin the Hage na Holand, wakilai daga ƙasashe fiye da 70 na duniya da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka shirya zaman taro a game da Afghanistan.

Sannan mako mai zuwa, ƙasar zata kasance a ajendar taron Ƙungiyar tsaro ta NATO.

Tun shekara ta 2001, Amurika ta kifar da mulkin ´yan taliban a ƙasar Afghansitan.Daga wannan lokaci zuwa yanzu, ƙasashe membobin ƙungiyar tsaro ta NATO, da ma wasu ƙarin ƙasashe masu hannu da shuni sun aika tawagogin sojoji a ƙarƙashin rundunar tsaro ta ISAF.

A yayin da take bayyani a game da tallafin da Jamus ke badawa, wajen samar da zaman lafiya da kuma bunƙasa tattalin arzikin Afghanistan, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa tayi: ta la´akari da irin kyakkyawar rawar da muka taka a Afghanistan tun shekara ta 2002, ba zamu daina bada haɗi kai ba, ga yunƙurin samar da zaman lafiya.

A halin da ake ciki ƙasar Jamus na da sojoji 3.700 dake aikin samar da tsaro a yankin arewancin Afghanistan.A shekara da ta gabata, gwamnatin Tarayya ta ware tsabar kuɗi, fiye da euro miliyan 530, domin gudanar da wannan aiki.

Jamus na gudanar da aiyukan samar da zaman lafiya kafaɗa kafaɗa da harakokin inganta rayuwar jama´a, kamar yadda Ministan tsaro Franz Josef Jung ya nunar:A Afghanistan mun yi sa´ar ƙirƙiro da tsari irin na bigi sa bigi taiki tun shekara ta 2003.Baya ga arewancin Afghanistan mun faɗaɗa shi zuwa yankunan kudu da gabacin ƙasar a shekara ta 2006.

Ƙasar Jamus ta zuba kuɗaɗe masu yawa a Afghanistan, ta fannin gina makarantu , asibitoci da hanyoyin zirga -zirga.

To saidai duk da haka, babu wani cenji azo a gani da aka samu ta fannin kyauttata rayuwar talaka, musaman dalili da cin hanci da rashawa ,da suka yi ƙwai suka ƙyenƙyasa a wannan ƙasa.

sai kuma safara miyagun ƙwayoyi da ta zama ruwan dare.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, tayi kira ga gwamnatin Afghansitan su kara lunka ƙoƙari wajen yaƙi da wannan matsaloli.A ganina ya zama wajibi,hukumomin Afghanistan su ƙara himmantuwa wajen shinfida zaman lafiya ta hanyar magance matsalar ´yan fashi da kuma masu safara miyagun ƙwayoyi.

Jamus ke ,matsayin ƙasa ta ukku bayan Amrika da Engla,wajen yawan sojoji a Afghanistan, baya ga ayyukan tsaro da na bada taimakon raya ƙasa, sojojin Jamus na horra da jami´an tsaron ƙasar Afghanistan ta yadda zuwa gaba su da kansu za iya ɗaukar yaunin tabbatar da doka da oda, a wannan ƙasa dake fama da tashe-tashen hankula.

Saidai duk da faɗi tashin da ƙashen keyi na cimma zaman lafiya a Afganstan kungiyar Taliban nan cigaba da nuna turjiya a game da haka, shugaban ƙasar Amurika Barack Obama ya yanke shawara kara yawan sojoji , matakin da Jamus tayi lale marhabin da shi ta bakin ministan harakokin waje Frank Walter Steinmeir:

Mun yi matuƙar farin ciki, ga aniyar da shugaba Barack Obama ya ɗauka a game da Afghanistan, baya ga matakin soja ta ƙara yawan kuɗaɗen taimakon raya ƙasa.

A watanin baya, Majalisar Dokokin Bundestag ,ta ƙada ƙuri´ar amincewa a game da ƙara sojoji dubu ɗaya a Afghanistan, to saidai mafi yawan al´umar ƙasa na nuna adawa da kasancewar sojojin Jamus a cikin wannan rikici.

Mawallafi: Nina Werkhäuser/ Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu