1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ɓangarori 4 dake tallafawa shirin zaman lafiyar GTT

September 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuAZ

A yau bangarorin nan 4 dake daukar nauyin shirin samar da zaman lafiya a yankin GTT zasu gana a hedkwatar MDD dake birnin New York inda zasu tattauna akan babban taron tsakanin Isra´ila da Falasdinawa da Amirka ta kira a cikin watan nuwamba. Taron a MDD na matsayi wata dama ga bangarorin hudu wadanda suka hada da MDD, Amirka, Rasha da KTT domin jin rahoton farko na tsohon FM Birtaniya Tony Blair tun bayan nada shi wakili na musamman a cikin watan yuni. Tun a cikin shekara ta 2003 bangarorin 4 suka tsara wani shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa da ake yiwa lakabi da taswirar hanya. To amma shirin wanda ya tanadi kirkiro wata kasar Falasdinawa kafin shekara ta 2005, tuni ya ruguje. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta amince ta saki firsinonin Falasdinawa 90 a yau lahadi a wani mataki na karfafa guiwar shugaba Mahmud Abbas gabanin taron kolin na watan nuwamba.