1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyoyin tawayen Darfur a birnin Arusha

August 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuEn

A birnin Arusha na ƙasar Tanzania an shiga yini na 2 a na tantanawa tsakanin ƙungiyoyin tawayen yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Majalisar Dinkin Dunia tare da haɗin gwiwar ƙungiyar taraya Afrika su ka shirya wannan taro, da zumar cimma alƙibla ɗaya, tsakanin yan tawayen, wacce kuma za su yi dogaro da ita, a wani na daban da gwamnatin ƙasar Sudan.

Saidai shugaban ƙungiyar tawayen SLA Abdel Waheed Mohamed El Nur, wanda a halin yanzu ke birnin Paris na ƙasar France, ya umurci ƙungiyar sa ta ƙauracewa wannan taro, bisa dallilan da ya bayyana kamar haka.

………………………….

„Ƙungiyar mu ta SLA ba zata halarci wannan taro ba,na Arusha, domin har kullum gwamnati da yan Janjawid na ci gaba da hallka ɗaruruwan mutane a yankin Darfur.

Mun kai koke ga ƙasashen dunia, mun roƙe su, su dakatar da wannan bila´i.“

A nata ɓangare gwamnatin ƙasar Sudan ta hiddo wata sanarwar a yau asabar, inda ta nuna shakku, a game da sahihancin shiga tsakanin France a rikicin Darfur.

Fadar mulkin Khartum tace,akwai lauje cikin naɗi, ta la´akari da yadda hukumomin France, su ka kasa shawo kan Mohamed An- Nuhr wanda ke birnin Paris domin ya halarci taron Arusha.