1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ƙungiyar Gamayyar Afirka

July 1, 2009

Cigaban tattaunawa a zauren taron ƙasashen Afirka

https://p.dw.com/p/If8M
Zauren taro a LibyaHoto: AP

A yau ne aka buɗe taron ƙoli na shugabanin ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Afirka. Ana saran mahallarta taron za su tattauna batutuwa da dama waɗanda suka haɗa da samar da wadataccen abinci da ruɗanin siyasa da ke a jamhuriyar Nijar.

Babban labarin da taron ya fara dashi, shi ne na ɗage takunkumin da ƙungiyar ta AU ta ɗorawa ƙasar Mauritaniya, wanda aka aza mata bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar. Yayinda harkar noma za ta kasance babban batu a wannan taron.

A jawabin buɗe taron jagorar ƙungiyar ta AU kuma mai masaukin baƙi shugaba Mu'ammar Gaddafi, cewa yayi wannan taron kamata yayi ya kasance na mussaman mai cike da tarihi a kudurin haɗin kan ƙasashen ƙungiyar da ake son cimma.

Shi ma da yake tsokaci Minista kula da Afirka da Asiya da Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙasar Burtaniya Lord Malloch-Brown, ya bayyana irin nassarorin da Tarrayar Afrika ta samu.

Gaddafi auf offiziellem Besuch in Italien
Moammar GadhafiHoto: picture alliance / dpa

"Ina ganin akwai hasashe masu yawa ga ƙasashen Afrika, ta wajen cuɗe ni in cuɗe ka da kuma kafa kasuwar bai ɗaya da suke yunkurin yi, wanda ke kama da ta Turai. Idan kayi misali da sauran nahiyoyi, suna gudanar da kasuwar bai ɗaya amma a nahiyar Afrika zancen ba haka yake ba. Bai fi kashi biyar cikin 100 na ƙasashen Afrika ke sayarwa makobtansu kaya ba, muna so mu sauya hakan. Ana bukatar samun haɗin gwiwa wajen harkar kasuwa, da tattalin arziki da kafa haɗaɗɗiyar ƙungiyar jami'an Kostom da dai sauransu. Kana kuma akwai bukatar ƙasashen Afrika suna kera kayan da makobtansu ke bukatar saye, ba wai su riga fitar da shi izuwa wassu nahiyoyi ba"

A taron na kwanaki uku dai shugabannin ƙasahen na da babatutuwa da dama wadan da zasu tattauna, kama daga yunkurin tazarce a jamahuriyar Nijar wanda ya jefa ƙasar cikin ruɗani, sai kuma sammacin da kotun duniya ta yiwa shugaban ƙasar Sudan, da halin da ake ciki a somalia, inda ake son ƙasashen ƙungiyar da su aika da karin dakarun tsaro. Da yake jawabi sakataren ƙungiyar ƙasashen larabawa Ammar Moussa ya jaddada muhimmancin samun haɗin kai tsakanin ƙasashen larabawa da ƙungiyar ta AU wajen warware matsalolin da suke damun su. Moussa ya ce kasancewa kimanin kashi 80 na yan Afrika sunfi dogara ne kan fannin noma, to dole a nemi hanyar ingantata.

Libyen Sirte AU Gipfel Muammar Gaddafi
Tutocin ƙasashen AfirkaHoto: AP

Shi kuwa shugaban ƙasar Brazil Lula da Silva wanda ya hallarci taron, kira yayi ga ɗaukaci ƙasashen ƙungiyar ta Tarrayar Afrika, da su yi Allah wadai da juyin mulkin ƙasar Hondurus, kuma suyi watsi da sabon shugaban har sai an mai da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar wanda ya yi yunkurin tarazce kafin sojojin ƙasar su sashi a jirgi suka fitar da shi daga cikin ƙasar.

An soke zuwan shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadijad wanda ake zaton halartarsa, da ma shugaba Gaddafi ne ya gayyace shi duk da adawar da ƙasashen yamma ke yi da Tehran.


Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed