1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arab League ta fara taron ƙoli a birnin Syrte

March 27, 2010

shugabanin ƙasashen larabawa sun fara taron ƙoli karo na 22 a birnin Syrte na Libiya tare da bada goyan baya ga Palestinu a rikicinta da Isra´ila.

https://p.dw.com/p/Mfyr
shugabanin ƙasashen larabawa sun haɗu a LibiyaHoto: AP

Shugabanin ƙasashen larabawa sun buɗa zaman taron ƙoli karo na 22 a birnin Syrte na ƙasar Libiya.Shugabanin sun yi amfani da wannan dama, domin bayyana matsayin bai ɗaya na takawa Isra´ila  birki, game da gine ginen da ta fara a gabacin birnin Qudus.

A jawabin da yayi ga wannan taro Sarkin Qatar Sheik Hamadi bin Khalifa al-Thani, ya bayyana takaici ga rabuwar kanun da ake samu tsakanain ƙasashen larabawa, wanda a cewarsa itace ta ba yahudawa damar cin karensu babu babbaka a Palestinu, to saidai a wannan karo bisa dukan alamu larabawan zasu ba maraɗa kunya kamar yadda ministan harakokin wajen Yamal al Quirby yayi bayyani:

"Gaba ɗaya mun amince da cewar hanya daya tilo da zata kaiwa ga zaman lafiya itace Isra´ila ta dakata gine gine da take a Palestinu.Idan ba haka ba,duk wani batu na zaman lafiya bai taso ba, kuma yankin ne gaba ɗaya zai fada cikin yanayi maras tabbas."

Sakatare Janar na Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa Amr Musa, ya bayyana alamun kasa cimma nasara, a sabon yunƙurin tattana rikicin Gabas ta tsakiya, saboda haka yayi kira da babbar murya ga shugabanin larabawa su kwan da shirin ɗaukar mataki mai ƙarfi ga Isra´ila.

Taron da shugaban ƙasar Libiya Mohamar Ƙhaddafi ke jagorata, ya samu halartar Firaministan Italiya Silvio Berlusconi a matsayin ɗan kallo.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Zainab Mohamed Abubakar