1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

291010 EU-Gipfel Abschluss

October 29, 2010

Shuagabannin ƙungiyar tarayyar Turai sun cimma daidaituwa akan yi wa yarjejeniyar gamayyar kuɗin Euro gyaran fuska

https://p.dw.com/p/PuDF
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

A yau juma'a shuagabannin ƙungiyar tarayyar Turai sun hallara a birnin Brussels na ƙasar Belgium domin sake yi wa yarjejeniyarsu ta gamayyar takardun kuɗin Euro kwaskwarima da cike giɓin dake tattare da yarjejeniyar tare da ƙara tsaurara matakan ladabtarwa akan ƙasashen da yawan fama da giɓin kasafin kuɗinsu.

Tun dai bayan da ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin Euro suka fuskanci barazana game da darajar takardun kuɗin na Euro sakamakon fatarar da ta rutsa da ƙasar Girka, shuagabannin ƙasashen ƙungiyar suka dace akan ba zasu yarda su riƙa tsaya wa ƙasashen dake fuskantar barazanar fatara ba. A zauren taron ƙolin na Brussels, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu nasarar tilasta aiwatar da wani canji ga yarjejeniyar haɗa-ka ta Kungiyar Tarayyar Turai da aka fi saninta da sunan yarjejeniyar Lisbon a taƙaice. An saurara daga bakin shugabar gwamnatin ta Jamus tana mai faɗi cewar:

"A yanzu takardun kuɗinmu na Euro na da kyakkyawar makoma sakamakon abubuwan da muka cimma a zauren wannan taro. Kuma a yanzun zai iya komawa gida gabana gaɗi."

A dai halin da ake ciki yanzu ƙasashe 16 daga cikin ƙasashe 27 na ƙungiyar tarayyar turan ne ke cikin inuwar gamayyar takardun kuɗin na Euro. Wasu daga cikinsu a halin yanzu haka suna fama da gwagwarmaya da ɗimbim bashin dake kansu, kamar dai Irland da Spain da Portugal da Italiya, a baya ga uwa-uba ƙasar Girka. Tun daga tsakiyar shekara mai zuwa sabuwar yarjejeniyar ta gamayyar takardun kuɗin Euro zata fara aiki. Sai kuma Angela Merkel ba ta samu nasarar cimma biyan dukkan buƙatunta ba. Ta fuskanci adawa daga shugaba Sarkozy na Faransa dangane da shawarar da ta bayar na ƙayyade ƙuri'ar duk wata ƙasar dake da ɗimbim bashi kanta. Merkel ta ƙara da cewa:

"Ba dukkan ƙasashen ne ke goyan bayan shawararmu ba, amma duk da haka wajibi ne mu yi wa yarjejeniyar gyaran fuska muddin muna sha'awar ƙirƙiro wani ƙwaƙƙwaran mataki na tinkarar duk wata matsala da ka taso. Idan kuwa har yarjejeniya na buƙatar canji to kuwa tilas ne a aiwatar da wannan canjin in kuwa ba haka ba abubuwa ba zasu tafi yadda ake buƙata ba."

A sabon matakin dai kamata yayi a shigar da asusun ba da lamuni na IMF da sauran bankuna masu zaman kansu ta yadda ba za a tsawwala al'amura akan masu biyan haraji da zarar wata ƙasa ta ƙungiyar ta fara fuskantar barazana ba. Hakan na nufi ke nan ƙungiyar tarayyar Turai ta koyi darasi daga abin rikicin kuɗin da aka fuskanta zamanin baya. A baya ga maganar yarjejeniyar ta takardun kuɗi kazalika shuagabannin sun tattauna maganar kasafin kuɗin ƙungiyar dangane da shekara mai kamawa da shirye-shiryen taron ƙolin gamayyar G20 a Seoul watan nuwamba mai zuwa da kuma taron yanayin da za a gudanar a Cacun ta Mexiko a wajejen ƙarshen shekara.

Mawallafi:Susanne Henn/Ahmad tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi