1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin EU da ƙasashen Latinamirka

Riegert, Bernd / Lima (DW Brüssel) May 15, 2008

Shugaba Hugo Chavez ke ɗaukar hankali dangane da furuce furucensa na tsokana

https://p.dw.com/p/E0HO
Merkel da ChavezHoto: AP

A yau ake buɗe taron ƙolin kwanaki biyu tsakanin ƙungiyar tarayyar Turai da ƙasashen yankin Latinamirka a birnin Lima. A taron na bana kamar wanda ya gudana a birnin Vienna a shekara ta 2006, shugaban Venezuella Hugo Chavez ya fi ɗaukar hankali inda ban da sukar da yake yiwa Amirka da ƙungiyar EU, a wannan karon ya juya kan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel inda ya kwatantata da shugaban ´yan Nazi Adolf Hitler. Mohammad Nasiru Auwal na ɗauke da ƙarin bayani...


Duk da wasa da hankalin jama´a da yayi da farko, yanzu shugaban Venezuela na daga cikin shugabannin dake halartar taron ƙolin ƙasashen Latinamirka, Karibiyan da kuma na Turai a birnin Lima. Taron a babban birnin ƙasar Peru shi ne karo na biyar da ya haɗa shugabannin ƙasashe 56 na Latinamirka da EU. A cikin wani shirin telebijin a ƙarshen mako shugaba Hugo Chavez mai ra´ayin gurguzu ya ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel mai ra´ayin mazan jiya tana da kusanci da Adolf Hitler. Duk da haka kakakin Merkel bai nuna damuwa ba domin ai furuta kalaman tsokana daga shugaba Chavez ba sabon abu ba ne. Angela Merkel wadda yanzu haka ta ke ziyara a yankin kudancin Amirka ta yi nuni da cewa shugaba Chavez ba zai iya zama kakakin sauran ƙasashen Latinamirka ba. Kamar dai a taron ƙolin da ya gudana a Vienna shekaru biyu baya a wannan karon ma shugaba Chavez da wasu shugabanni masu ra´ayin gurguzu daga Boliviya da Ecuador da ma Cyprus zasu gudanar da wani taro da suka kira wai taron jama´a a daura da taron ƙolin na EU da Latinamirka. Kwamishinar EU mai kula da hulɗoɗin ƙetare Benita Ferrero-Waldner ta yi fatan cewa fito na fito da za´a yi tsakanin ´yan gurguzu da masu ra´ayin mazan jiya ba zai dabaibaye manufar shirya taron ba wato yaƙi da talauci da sauyin yanayi.


Ferrero-Waldner: Ta ce "Ba za mu hana Chavez shirya wani taron ƙoli a gefen wannan taron ba, domin muna cikin wata duniya ce ta ´yancin da walwala."


A gefen taron na birnin Lima za a yi ƙoƙarin yin sulhu a rikicin da ake yi tsakanin Kolombiya da Ecuador dandane da ´yan tawayen ƙungiyar FARC masu ra´ayin gurguzu. Gabanin ta tashi daga Berlin zuwa taron shugabar gwamnatin Jamus ta yi kira ga ƙasashen Latinamirka da su ƙara ba wa juna haɗin kai a batutuwan da suka shafi duniya baki ɗaya.


Merkel ta ce "Mun san cewa sau da yawa saɓani da koƙarin kare buƙatun kai su kan mamaye batun hulɗar cinikaiya. Saboda haka a matsayi na na shugabar gwamnati zan yi amfani da taron ƙolin EU da ƙasashen Latinamirka don neman mun haɗe bukatumnmu wuri ɗaya."


Ita dai ƙungiyar EU na son a yi amfani da taron wajen tsara yadda nahiyoyin biyu zasu yaƙi sauyin yanayi da bunƙasa aikin noma tare da cimma matsaya ta bai ɗaya game da harkokin kasuwancin duniya. EU dai na matuƙar sha´awar ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da ƙasashen Latinamirka sannan ta na son ta rage yawan angizon da China ke samu a wannan yanki musamman a fannin kasuwanci da zuba jari. Sannan su kuma kasashen yankin kamar Peru suna son su ƙara yawan kayan da suke sayarwa nahiyar Turai tare da janyo hankalin kamfanonin Turai masu zuba jari.