1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin ƙungiyar G8

June 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuJe

Shugabanin ƙasashe masu cigaban masanaántu na duniya G8 sun hallara domin fara taron su da zai gudana a birnin Heiligendamm a nan Jamus. Ana sa ran shugabanin na G8 waɗanda suka haɗa da ƙasashen Britaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Rasha da kuma Amurka za su tattauna batutuwa na harkokin ƙasashen ƙetare wanda ya haɗa da shirin nukiliyar Iran da halin da ake ciki a Sudan da kuma rikicin Israila da Palasdinawa. Sai dai kuma ga alama taƙaddamar dake faruwa tsakanin shugaban Amurka George W Bush dana Rasha Vladimir Putin kan batun kafa kariyar makamai masu linzami a nahiyar turai ka iya mamaye muhawara a zauren taron sabanin batutuwan sauyin yanayin muhalli da kuma yaƙi da talauci a nahiyar Afrika waɗanda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel take ƙoƙarin bada fifiko a kan su.