1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin Ƙungiyar AU a Banjul

Yahouza Sadissou MadobiJuly 1, 2006

Shugabanin ƙasashen Afrika sun buɗa zaman taro a birnin Banjul na ƙasar Gambia

https://p.dw.com/p/BtzT

A jiya asabar ne, Ƙungiyar gamayyar Afrika wato AU, ta buɗa zaman taron yini 2, a birnin Banjul na ƙasar Gambia, taron da ya samu halartar kussan ɗaukacin shugabanin ƙasashen Afrika, da kuma Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan.

Shugaban ƙasar Gambia ne, Yahya Jammey mia masaukin baƙi, ya gabatar da jawabin buɗe wannan taro, wanda shine na 7,a tarihin ƙungiyar gamayar Afrika.

Sannan sakataran zartaswa, na AU Alfa Omar Konare , ya bayyana dalla dalla, ajendar taron, wanda ke tantanawa yanzu haka, a kan matsalolin da Ƙungiyar ke fuskanta, da kuma wajibcin lallubo matakan magance su cikin gaggawa.

Alfa Omar Konare, ya yi kira da babbar murya, ga shugabanin Afrika da su maida himma, wajen kawo ƙarshen rikicin Somalia, da na yankin Darfur,da ke ci gaba da hadasa asara rayuka.

Ya ce wajibe ne, ƙasashen Afrika su matsa ƙaimi ga ɓangarori masu gabada juna, a darfur, domin su yi aiki da yarjejeniyar zaman lahia,da su ka ratabawa hannu a birnin Abuja na Taraya Nigeria.

Sannan shugaba Omar El Bashir na Sudan, ya amince da karɓar tawagar dakarun shiga tsakaki na Majalisar Ɗinkin Dunia, domin maye gurbin sojojin ƙungiyar AU da ke fama da ƙarancin kuɗaɗen tafiyar da ayyuka.

Konare, ya gayaci shugabanin Afrika, su ba da haɗin kai, ga yunƙurin shinfiɗa demokradiyar, a Cote d´Ivoire da Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ƙasashe 2, da ke fama da rigingimmun tawaye, inda kuma aka tsara shirya zaɓuka a wannan shekara.

A yanzu haka, mahalarta taron, na ci gaba da tantanawa a game da matsalolin baƙin haure da kuma batun gurfanar da tsofan shugaban ƙasar Tchad Idriss Deby, gaban kotun ƙasar Belgium agame da zargin da a ke masa na aikata kissan kiyasu, ga jama´a, a zamanin mulki sa.

Komitin ƙurrarun masu shari´a, na Afrika, da AU ta umurci gudanar da tunani akan al´ammarin sun bada shawara gurfanar da Hissen Habre a kotunan Afrika, a maimakon na ƙasar Belgium.

A nasa jawabi, sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya ce yayi murnar ganin yadda a halin yanzu Afrika ta shiga gadan gadan, bisa tafarkin Demokradiya, bayan samun yanci kai, da kuma mulkin kama karya, a shekarun da su ka gababata.

Kazalika ya yaba yadda sannu a hankali a ke samun ci gaba da fannin habaka tattalin arzikin da kuma kare kaƙƙoƙin bani adama a nahiyar Afrika.

To saidai duk da wannan nasarori, har yanzu akwai sauran rina kaba inji Koffi Annan,ta la´akari da yadda cuttutuka, kamar su ƙanjamau, da kuma yinwa da rashin aikin yi ga matasa, su ka zama ƙayar wuya ga ƙasashen Afrika.

Sannu ba ta hannu zuwa inji sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, muddun Afrikawa suka maida himma, za a wayi gari watarana, su kasance cikin wadata ta hanyar tattalin arziki, ƙoshin lahia da kuma walwala.

Duk da cewar, zan bar kujera ta, a Majalisar Ɗinkin Dunia, ku tabbatar da ina tare da ku, a gwagwarmayar hidda surhen Afrika daga ruwa.

Taron na Birnin Banjul da za a kamalla nan gaba a yau, ya samu halartar shugaban Ahmadi Nedjad na ƙasar Iran, da kuma shugaban Hugo Shavez na Venezuela, ƙasashe 2,wanda babu ga maciji tsakanin su da Amurika.