1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli tsakanin shugabannin ƙasashen Koriyawa biyu

October 3, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9g

Shugaban KTK Roh Moo-Hyun da takwaransa na KTA Kim Jong-Il a hukumance sun fara gudanar ta tattauawar su ta farko cikin shekaru 7. Shugaba Roh ya ce yana son yayi amfani da taron koli a matsayin wani sharadin farko na samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin tsibirin Koriya. Ya ce taron zai kuma taimaka wajen rage hauhawar tsamari tsakanin kasashen biyu tare da habaka tattalin arzikin KTA mai bin tsarin kwaminisanci. Shugaba Roh wanda sauran watanni 5 wa´adin shugabancin sa ya kare ya ce zai nema da a sanya hannu kan wata yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da KTA. A kuma halin da ake ciki kasar Amirka ta ce ta amince da wani shiri da aka cimma a lokacin shawarwarin kasashen nan 6 wanda ke da nufin lalata tashoshin nukiliyar KTA kafin karshen wannan shekara.