1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli tsakanin Angeller Merkel da Jacques Chirac

June 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuvD

shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkell, da shugaban ƙasar France Jacques Chirac, a garin Rheinsberg, da ke arewancin birnin Berlin.

Mahimman batutuwan da tawagogin 2, ke tantanawa a kai, sun haɗa da mattakan samar da masallahar shinfiɗa A ɗazun nan ne, a ka fara taron yini ɗaya tsakanin daftarin tsarin mulki, na ƙungiyar gamayya turai, bayan da ƙasar France, ta yi watsi da shi,a shekara da ta gabata.

Sannan, za su masanyar ra´ayoyin a game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, a sakamakon matakin da Amurika ta ɗauka, na shiga cikin tanttanawar.

A ɗaya hannun, Merkel da Chirak, za su cenza miyau, a dangane da Jamhuriya Demokradiyar Kongo, bayan da ƙungiyar EU,ta amince, ta tura dakaru a wannan ƙasa, domin sa iddo, ga zabbukan da za a gudanar, a ƙarshen wata mai kamawa.