1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli tsakanin Afrika da EU a birnin Berlin

May 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuKs

Shugabar gwamnatin Jamus bugu da ƙari shugabar ƙungiyar gamayya turai Angeller Merkel, ta buɗa taron tantanawa karo na 8, tsakanin EU da ƙasashen Afrika a game da hanyoyin yaƙi da talauci ,a wannan nahiya.

Wannan taro na yini 2, ya samu halarta shugabar ƙasar Liberia Elen Sirleaf Johson da tawagogi daga sassa daban-daban na dunia.

A tsawan yini 2, mahalarta taron,za su mahaurori a game da mattakan bai ɗaya, na yaƙi da talauci a Afrika, wanda za su gabatar wa shugabanin ƙasashe G8, ataron da su shirya nan da makwani 2, a nan ƙasar Jamus.

Angeler Merkel, ta alƙawarta tuntubar takwarorin ta na G8, domin su ƙara dubin Afrika da idon Rahama, ta fannin bada taimakon raya ƙasa.

Shugabanin ƙasashe 9, na Afrika, da su ka haɗa da Umaru Musa Yar Aduwa, na Nigeria, da John Kuffor na Ghana, za su halarci taron na G8 da a za a shirya a nan ƙasar Jamus a wata mai kamawa.