taron ƙoli na Majalisar Ɗinkin Dunia a New York
September 19, 2006Talla
A birnin New York na kasar Amurika, an ci gaba da tantanawa tsakanin shugabanin Kasashen dunia a game da riginginmun da ke wakana a duniayar ta mu.
Shugabanin sun hadu albarkacin taron kloli na kasasshe membobin MDD.
Shugaban kasar France Jacque Chirak da Sakatare Jannar na MDD Koffi Annan, sun tantana a game da matakan maido da zaman lahia,a yankin kinta ganas ta tsakiya, mussamman a rikicin da ya ki ci, ya ki cenyewa, tsakanin Isra´ila da Palestinu.
A ɗaya hanun, sun yi masanyar ra´yoyi, a game da halin da ake ciki a yankin Darfur na ƙasar Sudan, inda su ka cimma matsaya ɗaya, a kan wajibcin tura dakarun shiga tasakani cikin gaggawa.