1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli na EU da AU

November 29, 2010

Gaddafi ya yi kira ga Tarayyar Turai ta ba da da tallafi wajen rage kwararar baƙin hauren da ke bi ta Libiya suna shiga Nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/QLMM
Shugaban Libiya Moammar Gadhafi, dama, yana gaisawa da shugaban hukumar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy a yayin da ake ƙaddamar da taron ƙolin a TripoliHoto: AP

Wakilan ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ƙasashen Tarayyar Turai waɗanda suka haɗa da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da Firaministan Italiya Silvio Berlusconi sun haɗu a Tripoli, babban birnin Libiya inda ake gudanar da taron ƙoli na tsawan kwanaki biyu, tsakanin ƙungiyar Tarayya Afirka da ta EU.

Mahimman batutuwan da taron ke tattanawa akai, sun hada da  samar da hanyoyin ci-gaban Afirka, kyautata hulɗar cinikayya da kuma kwararowar baƙin haure zuwa Turai.

A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa na buɗe taron, shugaban Libya Moammar Gaddafi wanda ke karɓar baƙuncin taron, ya ce ya kamata Tarayyar Turai da bada aƙalla Euro billiyan biyar domin magance matsalar baƙin hauren da ke bi ta Libiya domin shiga Turai. Ya kuma bayyana cewa Libiya ta yanke shawarar hukunta baƙin hauren da aka kama. A watan da ya gabata an ware miliyoyin kuɗaɗe domin samar da nauroin da za su iya hangen mutane daga nesa, wanda zai taimaka wajen gano mutanen da ke fakewa a gaɓar tekun.

Ita dai Tarayyar Turai, tana ba da fifiƙo ne akan hanyoyin samar da aiki da zuba jari da kuma bunƙasar tattalin arziƙi.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Mohammad Nasiru Awal