1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli na ƙungiyar AU a birnin Accra

July 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuHI

Albarakacin taron ƙoli karo na 9, da su ka ƙaddamar a birnin Accra na kasar Ghana, shugabanin ƙasashen Afrika, sun tabka mahaurori a game da batun haɗe Afrika a matsayin ƙasa guda.

Shugaba Muhamar Ƙhadafi na Lybia,, da takwaran sa Abdu Diouf, na Senegal, ke gan gaba, a jerin shugabanin Afrika da ke da wannan muradi, a yayin da shugaban Afrika ta kudu Tabon Mbeki, na matsayin mai adawa da matakin.

A nasa gefen shugaba mai mai saukin baki John Kufor ya nunar da mahimancin girka haɗɗaɗiyar gwamnatin Afrika, amma da sharaɗin shinfiɗa matakan cimma burin da aka sa gaba.

A daya wajen ,Shugabanin Afrika, sun tabka mahaurori a game da tashe-tashen hankulla da ke wakana a wasu ƙasashen nahiyar , mussaman a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

To saidai a na yi wannan mahaura, ba tare da halaratar shugaban ƙasar Sudan ba, Omar El Beshir.

A jawabinda ya gabatar,Shugaban hukumar zartzaswa ta ƙungiyar taraya Afrika, Alfa Omar Konare, ya yi tur da Allah wadai, ga harin da wasu mutane ɗauke da manyan makamai, su ka kai wa Praministan Cote D´Ivoire Guillaume Soro ranar juma´ada ta wuce.