1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

220909 Brasilien Afrika

September 27, 2009

Alaƙa tsakanin ƙasashen kudancin Amurka da takwarorinsu na Afirka a fannoni daban daban ciki har da na kasuwanci.

https://p.dw.com/p/Jq3t
Ƙarfafa dangantaka tsakanin Latinamirka da AfirkaHoto: AP

Ƙasashen dake kudancin Amurka nada alaka ta kut da kut da takwarorinsu na Afirka a fannin kasuwanci, wanda hakan ne ya jagoranci gudanar da taron yini biyu a karo na biyu tsakanin ɓangarorin biyu daga ranar asabar 26 zuwa 27 ga watan Satumba a birnin Isla de Margarita dake ƙasar Venezuela.

Brazil dake zama ƙasa mafi karfin tattalin arziki a yankin Latin Amirka dai a yanzu haka, tana daɗa samun bunƙasa, inda tuni ta ja hankalin ɗaya ɓangaren yankin Atlantika.

A ƙarƙashin jagorancin shugaba Luiz Lula da Silva dai tuni ƙasar ta faɗaɗa harkokin kasuwancin ta zuwa nahiyar Afirka. Manufar gwamnatinsa dai shi ne ta ga cewar ta yi tasiri a harkokin kasuwanci na wannan nahiya.

Tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadagon dai na fatan ganin ingantuwar dangantakar kasuwanci da wasu ayyukan raya ƙasashe masu tasowa da matalauta, kamar yadda yayi bayani a taron kasuwanci na Majalisar Ɗunkin Duniya a shekara ta 2004, a birnin Sao Paulo.

"Wannan sabon yanayi ba ya nufin sauya harkokin kasuwancin Arewaci da Kudanci. Zamu cigaba da darajawa abokan kasuwancinmu na Arewaci da suka cigaba, kuma hulɗoɗinmu zasu cigaba. Muna farin ciki da inda kayayyakin mu suke kaiwa a ƙetare, da ma wuraren zuba jari, kuma muna la'akari da amfani da ingantattun fasahohi na zamani. Amma duk da haka muna muradin buɗe wata kafa ta samar da dama da kuma dangantaka da ƙasashen dake kudanci, domin taimakawa bunƙasar tattalin arzikin ɓangarorin biyu."

Daga nan dangantakar ta fara, inda yanzu haka Brazil na sayar da mafi yawan kayakin da take sarrafawa ga ƙasashe masu tasowa da matalauta, fiye da na Arewaci.

Yanzu haka dai Sin ita ce ƙasa ta uku da Brazil ke hulɗar kasuwanci da ita, a bayan Amurka da makwabciyarta Argentina, wanda matsayinsu ke neman zama daidai.

Bayan Ƙasar Sin dai, nahiyar Afirka ce kamfanonin Brazil suka mayar da hankali akai, nahiyar da taka rawa a zamanin cinikin bayi a Brazil.

Shugaba Lula da Silva na Brazil dai ya kai rangadin aiki daban-daban har sau 11 a nahiyar Afirka, bisa la'akari da cewar ƙasarsa ce take ɗauke da mafi yawan baƙaƙe bayan nahiyar Afirkan ita kanta. Kazalika shi ma kamfanin tallata kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙetare, ya mike tsaye domin yin tasiri a Afirka. Inda a watan Satumban bara ne, tawagar jami'an kamfanin suka ziyarci abokan kasuwancinsu dake ƙasar Afirka ta kudu. Mauricio Manfred shine shugaban hukumar ta APEX.

"Manufarmu shine, ƙarfafa tare da inganta wannan dangantaka. Ba wai muna wakiltan kamfanonin Brazil ne kaɗai ba, amma harma da kayayyakin da zamu iya shigarwa ƙasarmu. Muna neman sabbin hanyoyin kasuwanci ne, musamman a yanzu da Duniya take cikin matsaloli na tattalin arziki."

A shekaru 10 da suka gabata dai, Brazil ta cimma shigar da kayayyakinta zuwa ƙasashen nahiyar Afirka dake yankin Sahara. A bara kaɗai, ta fitar da kayayyakin ta na wajen kashi biyar daga cikin 100 da kuɗinsu ya kai dalan Amurka biliyan 10. Daga wannan adadi dai, Angola ce ke kan gaba a ciniki da Brazil da wajen dala biliyan biyu, sai Afirka ta kudu 1.8. sai kuma Nigeria da kimanin dala miliyan guda da rabi.

Mawallafa: Johannes Beck/Zainab Abubakar

Edita: Mohammad Nasiru Awal