1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen duniya domin taimakawa Somaliya wajan tabata da zaman lafiya

May 22, 2010

Ƙasashen duniya na gudanar da wani taro a birnin Istambul domin taimakawa ga samar da zaman lafiya a ƙasar Somaliya

https://p.dw.com/p/NUtD
Taɓarɓarwa al'amuran tsaro a ƙasar somaliyaHoto: AP

  Wakilai na gwamnatoci da shugabannin ƙasashen 55 na ƙasashen Afirka da yanki Asiya, da na Turai haɗe da mayan ƙungiyoyi na duniya da ke yin taro a birnin Istambul ,sun jadada aniyarsu ta kawo ɗauki ga hallartaciya gwamnati  riƙon kwarya ta ƙasar Somaliya


Da ya ke jawabi a wajan bude taron sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon, ya ce babbar hanyar da za ta zama ma fi a-Ala wajan sake dawo da kwanciyar hankali a ƙasar ta Somaliya, ita ce ta taimakawa gwamnatin akan yunƙurinta na sake sasanta tsakanin al-umar ƙasar, tare da yin yaƙi da yan aware .


Gwamnatin dai ta ƙasar Somaliya wace ke da taƙaitacen iko da birnin  Mogadishio, na kan hanyar ƙara samu agajin ƙasashen duniya wajan sake kwato ƙasar daga hannu masu fafatikar kishin adinin islama



Mawallafi  :Abdourahamane Hassane

Edita         : Zainab Mohame abubakar