1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen duniya akan harakokin tsaro

April 13, 2010

Taron Amurka kan rage yaɗuwar makaman nukliya a duniya

https://p.dw.com/p/Muv3
Shugaban ƙasar Amurka a wajen taron rage yaɗuwar makaman nukliyaHoto: AP

Shugaba Obama ya yi gargaɗin da a yi hatara ga guri yan ta'ada na kai ga sa hannu akan makaman ƙare dangin na nukliya,mista Obama da ke magana a sa'ilin buɗe taron ƙolli da ƙasarsa ta karɓi bakoncinsa, ya ce  a kwai barazana ta ƙungiyar  al-qäida da ya kamata tun yanzu a ɗau matakan gaugawa.

Taron wanda shine irinsa na farko tun a shekara ta 1945 da Amurka ta shirya ,wanda ya samu halarta shugabani da dama,Shugaban ƙasar na Amurka yayi amfani da wannan damar domin tunasar da shugabannin ƙasashen duniya da su tanadi matakai na kariya ga ma'adinai na uraniun wanda da sune ake kera makamin atom domin kada su kai cikin hannu yan ta'adar.

Yanzu haka dai akwai tonne kimani 1600 na uranium da tonne 600 na sinadarin plutonium a cikin duniya wanda  su kaɗai sun isa a ƙera  bam120000 da su ,wanda haryanzu hukumar samar da makamashi ta duniya bata karfin yin kariya akan su.

Dangane da yadda aka fara samu fataucinsu wanda aka kiesta cewa kamar so 15 aka samu yin fasa ƙoɓri sinadaren tun da ga shekara 1993 zuwa shekara 2008 musammunma a yanki tshofuwar taraya Soviet  ..

Shugabannin ƙasashen duniyar da ke kokarin daidaita matakai na rage yaɗuwar makamai na nukliya, na kan hanyar samun faimtar juna wajen sake sakawa ƙasar Iran takunkumi karya tatalin arziki, to sai dai haryanzu ƙasar China ta fi bada fifiko da a bi hanyoyin diflomasiya na tataunawa domin warware ta'adamar ,yayin dakuma shugaban ƙasar Faransa Nikola Sarkozy ya baiyana cewa ƙasarsa ba a shirye ta ke ba ta yi watsi da shirin kera makamai na nukliya saboda dalilai na tsaro.

Mawallafi:Abdourahamane Hasssane

Edita       :Abdullahi Tanko Bala