1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen Afrika a game da matsalar baƙin haure

April 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2p

Wakilai daga kasahe 50 na Afrika sun kammala zaman taro a birnin Algers na kasar Algeria a game da batun kwarar Afrikawa daga kasashe su na assuli, zuwa sauran sassa na dunia mussaman turai.

Bayan mahaurorin da su ka gudanar, mahalarta taron sun cimma matsaya ɗaya, a game da matakan magance wannan matsala.

Babban mataki, a cewar su, shine na ƙara hanyoyin bada tallafi ga ƙasashen Afrika, ta fannin bunƙasa arziki.

A cikin sanarwar ƙarshe, da za su gabatarwa hukumar zartaswa, ta ƙungiyar tarayya Afrika, sun bada shawarwari na fita daga matsalar gudun hijira, da ta zama ruwan dare a Afrika.

Ministan kulla da harakokin Afrika da na Magreb na kasar Algeria da ya ke jawabin karshen taron ya tabatar da cewa, mattakan ƙarffafa tsaro da ƙasashen turai ke ci gada da ɗauka, a halin yanzu, ba su issa a ciwo kan matsalar.

An kiri wannan taro, a shirye shiryen babban taron da zai haɗa tawagogin Afrika da na turai, a ƙasar Liyba daga 5 zuwa 6 ga watan juni, domin tantana batun matsalolin gudun hijira.