Taron ƙasashen Afrika a game da citar Sida a birnin Brazaville
March 7, 2006A birnin Brazaville na Jamhuriya Afrika ta tsakiya, wakilai daga kasashe Afrika, tare da ƙurrarun ta fannin kiwon lahia, na ci gaba da zaman taro, a game da batun cutar Aids, ko Sida a nahiyar Afrika.
Hukumar Majalisar ɗinkin Dunia mai yaki da Aids ta gayyaci wannan taro na kwanaki 3.
Jawabai daban daban da a ka gudanar, sun bayyana rashin samun nasarar murƙushe wannan cuta.
Duk da magudan kuɗaɗen da Majalisar Ɗinkin Dunia, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ke sakawa a yaƙin, abun,ya zama tamkar a na magani kai na ƙaba, ta la´akari da yaɗuwar cutar kamar wutar daji.
Shugaban hukumar yaƙi da Sida, a Majalisar Ɗinkin Dunia Michel Sidibe,ya ce duk shekara ta Allah,a na samun ƙarin mutane million 3, a nahiyar Afrika, da ke kamuwa da cutar Aids, sannan tan a hallaka mutane kussan million 3 a ko wace shekara, a nahiyar Afrika, tare da barin marayu million 14 cikin.
Mahalarta wannan taro, sun shawarci sake shiri, da sake sallon yaƙi da cutar Sida a Afrika.