1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashe masu ci-gaban masana'antu

June 25, 2010

Shugabannin na ƙasashen ƙungiyar G8 sun soma tattaunawa a ƙasar Kanada

https://p.dw.com/p/O3Op
Hoto: AP

Shugabannin ƙasahe ƙungiyar G8 na ƙasahe masu ci-gaban masana'antu sun soma gudanar da wani taro a yau a birnin Huntsville, na ƙasar Kanada.

Taron wanda ake gudanarwa gabanin taron G20 na mayar da hankali ne kan butun samar da ci-gaba ga ƙasashen, da maganar shigar da haraji a cikin bankuna da dai sauran bututuwa masu mahimmanci da shugabanin ƙasashen Faransa da Rasha da Amurka da Jamus da Japon da Ingila da Italiya da kuma ƙasar Kanada mai masaukin baƙin zasu tattauna.

Shugabar gwamantin ƙasar Jamus, Angela Merkel na daga cikin shugabannin da ke hallarta taron.

Ta ce:"Ba na tsamanin za mu samu ra'ayi ɗaya kuma tilas ne na faɗi haka.

To amma ina ganin mu a matsayinmu na ƙasar Jamus zamu yi ƙoƙarin ba da ta mu gundunmuwa wajen warware wannan rikici na kuɗi da ake fama da shi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.

Edita : Halima Balaraba Abas.