1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashe da ƙungiyoyin masu hannu da shuni a Monrovia

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buqk

Ƙasashe masu hannu da shuni, da kafofin bada lamani na dunia, na ci gabada zaman taro a birnin Monrovia na ƙasar Liberia.

Shugabar gwamnatin Liberia Ellen Searlef Johson, da ta gayyaci wannan mahimmin taro, ta buƙaci ƙasashe da ƙungiyoyin, su yafe ɗimbin basussuka, da yawan su, ya kai dalla biliar dubu 3 da rabi,wanda su ka tambayo Liberia.

Sannan shugabar, ta tara ƙoƙon bara na neman taimakon ƙarin kudade, domin sake gina Liberia da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Ellen Searlef Johson ,ta bayana burin gina makarantu, da assibitoci, da kuma bada horo ga maluman makaranta.

Kazalika, Liberia na bukatar samun wutar lantarki, da tasbatatun ruwan sha cikin gaggawa.

Mahalarta wannan taro, da su ka haɗa da Ƙungiyar gammayar Turai, bankin dunia da assusun bada lamani na dunia, da kuma bankin ci gaban ƙasashen Afrika, za su anfani da wanna dama domin bitar nasara da sabuwar gwamnatin Liberia ta cimma watani 6 bayan girkuwar ta.