Taro tsakanin EU da Iran | Labarai | DW | 06.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taro tsakanin EU da Iran

Nan gaba a yau ne tawagar ƙungiyar gamayya turai, zata ganawa da ta ƙasar Iran, a game da rikicin makaman nuklea.

Da farko ,Jiya a ka tsara yin wannan haɗuwa , amma daga bisani, Iran ta ƙi amsa gayata, domin nuna fushi, a kann yadda EU, ke yawan haɗuwa da Maryam Radjavi,wani ɗan adawar ƙasar Iran, da ke gudun hijira.

Tawagogin 2, za su ci gaba da masanyar ra´ayoyi, a game da hanyoyin warware taƙƙadamar rikicin nukleya.

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana, da Ali Larjani, za su yi bitar inda aka kwana a wannan baddaƙala, bayan haɗuwar da su ka yi watan da ya wuce, a birnin Teheran.

Iran ta sannar cewa zata bada, ansa ga tayin da ƙasashen turai da Amurika su ka yi mata, kamin 22 ga watan Ogust mai zuwa.

To saidai, masana harakokin diplomatia na hasashen cewar, Iran zata ci gaba da tsayawa kan matsayin ta,na ƙera makaman nukleya, ta la´kari da rarabuwar kanu, da ake fuskanta a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia a kan wannan batu.