Taro kan muhimmancin yanar gizo wajen neman ilimi a Zambia | Zamantakewa | DW | 26.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taro kan muhimmancin yanar gizo wajen neman ilimi a Zambia

Yadda mazauna karkara ke cin gajiyar amfani da yanar gizo wajen inganta iliminsu

default

A karo na huɗu a wannan makon ƙwararru da masu sha'awar neman ƙarin ilimi ta yanar gizo a ƙasashen Afirka suka hallara a Lusakan Zambiya domin tattauna muhimmancin yanar gizo wajen neman ilimi. Kuma ko da yake ba a dukkan sassa na Afirka ne akan san wannan hanya ta neman ilimi ta yanar gizo ba, amma a wani ƙauye dake can ƙuryar ƙasar Zambiya tuni wannan manufa ta tabbata.

A tsakiyar ƙauyen Macha dake ƙuryar ƙasar Zambiya an anjiye wata babbar kwatena. Sai da aka buƙaci wasu ƙarfafan maza su shida da injin ɗaukar kaya domin sauke kwantenar daga babbar motar dake ɗauke da ita. A jikinta an rubuta taken: Sadarwa ta yanar gizo: Sadarwa tsakanina da maƙobcina ko kuma Linknet - Connecting my neighbour da turanci. Wannan manufar ita ce ainihin abin da ƙungiyar Macha Works ta yankin ta sa gaba. Domin kuwa a sakamakon ayyukan sadarwa ta yanar gizo ana samun kyakkyawan ci gaba a yankinGa dai abin da shugaban ƙungiyar Fred Mweetwa yake cewa game da irin ci gaban da aka samu a ƙauyen Macha:

 "Idan na duba irin ci gaban da aka samu game da yanayin rayuwar jama'a sai lamarin ya zama kamar mafarki ne a gare ni. Lokacin da na taso, a wani zubin ni kan yi yini huɗu ba tare da na ci ba, amma a yau na wayi gari a matsayin ɗalibi a jami'ar Afirka ta Kudu. Ina neman ƙarin ilimi ne ta yanar gizo. Ina amfani da ita wajen gudanar da bincike da tuntuɓar malamai na. Kai hatta ta waya ni kan samu ikon zaƙulo abubuwan da nike buƙa ta in kuma gabatar da ayyukan da aka danƙa mini. Duk hakan ta wayar tarfo."

Fred na kan hanyarsa ta zuwa Lusaka, babban birnin ƙasar Zambiya daidai da kwantenar da aka saka cikin babbar motar tare da komfutoci guda shida. Fred Mweeta zai yi amfani da su ne domin bayani akan ɓangaren fasaha game da shirin nasu a zauren taron.

Kimanin komputoci 200 ake adsu a yankin galibi a makarantu da asibitoci da kuma cibiyoyin bincike. Kuma duk wanda ba ya da wutar lantarki a gidansa yana iya tafiya zuwa internetcafe, wanda ba shi da btsada sakamakon tallafi na kuɗi da ake bayarwa. Shi ma asibitin Macha na da hanyar sadarwa ta yanar gizo, inda wani ma'aikacin asibitin mai suna Jonathan Sitali ya kan zauna, bayan ya sauka daga bakin aikinsa, domin kutsawa shafi yanar gizo na jami'ar Liverpool. Likitan na so ne ya nemi ƙarin ilimi akan kimiyyar kiwon lafiya a jami'ar. Ya ce kasancewar yana da abokan karatu a sassa daban-daban na duniya, wannan babban ci gaba ne gare shi...

"Ba wani babbanci a game da ko mutum na halartar aji ne ko kuma yana zaune ne shi kaɗai don karɓar darussa. Babban ci gaba a nan shi ne kasancewar an haɗa ɗalibai ne daga sassa daban-daban na duniya. Sannan na biyu kuma shi ne zan iya tafiyar da aiki na a matsayina na likita kuma a lokaci guda ina neman ƙarin ilimi."

Wani injiniya ɗan ƙasar Holland mai suna Gertjan van Stamm, shi ne ya ƙirƙiro shirin na Macha Workers ya kuma dasa tubalin farko na sadarwa ta yanar gizo tare da gangamin neman taimako daga 'yan kasuwa na Holland da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal Edita: Zainab Mohammed