1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARO KAN BUNKASA ILIMI A KASASHEN LARABAWA.

Yahaya Ahmed.February 11, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlx
Ministan kula da ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta nan Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta yi kira ga kasashen Larabawa da su tashi tsaye su huskanci kalubalen da duk sauran kasashen duniya ma ke ta fama da su, wato na yi wa tsarin kafofinsu kwaskwarimar da ta dace da sauyin zamani, don kyautata halin rayuwar al'ummominsu. Ministan ta yi wannan kiran ne a gun wani taron yini 2, da aka gudanar a birnin Berlin don tattauna matsalolin da kafofin yada ilimin kasashen Larabawa ke huskanta a halin yanzu, da kuma irin taimakon da Jamus za ta iya ba su. A cikin jawabinta ministan ta bayyana cewa:-
"Manufar da ta hada mu a gun wannan taron ita ce, ta cim ma gurin aiwatad da canje-canjen da suka zamo wajibi gare mu, wadanda kuma kundin nan na ARAB HUMAN DEVELOPMENT REPORT ya tsara don mu iya yin amfani da su."
Wannan kundin dai, masana fannoni daban-daban na kasashen Larabawa da Hukumar Raya kasashe Masu Tasowa ta Majalisar dinkin Duniya ne suka tsara shi. Kuma yana kalubalantar kasashen Larabawan ne da su tashi tsaye su nuna kwazo da bajinta wajen kau da shingayen da ke hana ci gaban al'ummominsu. Wadannan kuwa, sun hada ne da kare hakkin dan Adam, da bai wa mata damar taka rawar gani wajen inganta halin rayuwar jama'a da kuma yi wa kafofin ilimi kwaskwarima.
Batun yada ilimin kuwa, shi ne ya fi ci wa mafi yawan kasashen Larabawan tuwo a kwarya. An dai kiyasci cewa kusan manyan mutane miliyan 65 a kasashen ne ba su iya rubutu ko karatu ba. Akwai kuma kimanin yara miliyan goma, wadanda ba su taba halaratar wata makaranta ba. Wannan halin kuwa, na janyo illoli da dama ga tattalin arzikin kasashen Larabawan, inda a cikin shekaru 20 da suka wuce, ba a sami bunkasar tattalin arzikin da ta wuce kashi sifili da digo 5 ba, inji rahoton.
Matsalar dai ta bambanta ne daga kasa zuwa kasa, inji Dr. Rima Khalaf, shugabar reshen kasashen Larabawa na Hukumar Raya kasashe Masu Tasowa ta Majalisar dinkin Duniya. Dr. Rima, wadda ita ma ta halarci taron na Berlin, ta kara bayyana cewa:-
"Rahoton dai ya sami karbuwar kungiyoyi da kafofi da dama. Fannonin siyasa, da dalibai da jami'o'i sun nuna gamsuwarsu da shi. Haka kuma kasashen Jorrdan da Yemen. Wasu jami'o'in ma sun fara koyad da wasu darussan da rahoton ke dauke da su a azuzuwansu. Akwai dai kuma gwamnatocin da ba su yi amanna da rahoton da muka bugan ba. Amma idan muna son mu yi aikinmu kan gaskiya, ai dole ne mu buga duk sakamakkon da muka samu, ko da ma wasu bangarori ba za su ji dadin bayyana su da muka yi ba."
Ita dai ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta yi wa taron alkawarin cewa Jamus za ta ci gaba da ba da gudummuwa a fannin yada ilimi a kasashen na Larabawa. Tuni dai, inji ministan, Jamus ta kulla yarjejeniya da wasu kasashen Larabawan:-
"Mun fara gudanad da wasu shirye-shirye a Masar, da Jordan, da Lebanon, da Siriya, da kuma Yankin Falasdinawa. Kuma wannan aikin hadin gwiwar ya fi ba da karfi ne a fannonin yada ilimi da koyad da sana'o'i. Muna kuma da wani shiri na bunkasa ma'ammala tsakkanin jami'o'i na wadnnan kasashen."
A nan dai za a iya ambatar Jami'ar da Jamus ta kafa ne a birnin Al-kahira, ko kuma yarjejeniyar huldodi tsakanin kafofin yada ilimi mai zurfi da Jamus ta kulla da kasar Jordan. Irin wadannan huldodin ne Heidemarie Wieczorek-Zeul ta ce nan gaba za a kara fadada su.