Taro a kan matsalolin bakin haure a birnin Dakar | Labarai | DW | 06.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taro a kan matsalolin bakin haure a birnin Dakar

Ƙurrarun masana daga ƙasashe 50 na Afrika, da turai, sun buɗa taron yini 2, a birnin Dakar na ƙasar Senegal, a game da matsalolin yan gudun hijira, da ke kwarara daga Afrika zuwa ƙasashen turai.

Mahalarta wannan taro, na masanyar ra´ayoyi, a kan hanyoyin yaƙi da baƙin haure, da kuma neman matakan ciwo kan, dubunan matasan Afrikawa na zaunawa ƙasashen su na assuli.

Ƙasashen France, Spain da Marroko ne ,da su ka fi ɗanɗana kuɗar wannan matsala, su ka gabatar da daftarin da wannan taro ke mahaura kan sa.

Tantanawar na matsayin share fage, ga taron ƙolin minsitocin turai da Afrika da zai gudana, daga 10 zuwa 11 ga watan july mai zuwa, a birnin Rabah na ƙasar Marroko.

Baki ɗaya masu halartar wannan taro, sun yi na´am da cewar, muddum ba a ɗauki nagarttatun mattakai ba, na yaƙi da zaman kashe wado, fatara da talauci da su ka yi ƙwai su ka ƙyenƙensa, a nahiyar Afrika, akwai matukar wuya, a magance matsalolin baƙin haure.

Matakan da ƙasashen turai ke ɗauka na ƙarfafa tsaro, akan iyakokin su, ba za su taɓa kawo ƙarshen matsalar ba a cewar mahalarta taron.