1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin yakin kasar Kwalambiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 11, 2016

Don Allah inaso ku yi min cikakken bayani akan dalili da kuma san da aka fara rikicin tsakanin gwamnatin kasar Kwalambiya da kuma 'yan tawayen FARC.

https://p.dw.com/p/2R7iM
Kolumbien Präsident Santos
Hoto: Reuters/Colombian Presidency

Tambaya daga Mahmud Salihu Kaura Namoda a jihar Zamfarar Najeriya wanda yake cewa: "Don Allah inaso ku yi min cikakken bayani akan rikicin tsakanin gwamnatin kasar Colombia da kuma 'yan tawayen FARC. Shin a wacce shekara aka fara rikicin? Kuma minene sanadin rikicin? Ko an taba samun yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin bangarorin?"

Domin jinamasar wannan tambaya, na mika ta ga wakilinmu na jihar Kaduna a Tarayyar Najeriya Ibrahima Yakubu wanda ya tattauna da Farfesa Abdullahi Ashafa malami a jami'ar jihar Kaduna bangaren tarihi, ga kuma amsar da ya bayar dangane da tarihi da ma lokacin da aka fara wannan yaki:

Ashafa:

"Rikici tsakanin gwamnatin Kwalambiya da sojojin juyin-juya hali na kasar Kwalambiya wato FARC din, rikici ne da ya samo asali tun kusan shekaru 52 ke nan, wato tun shekara ta 1964, inda wani dan siyasa kuma dan gwagwarmaya mai suna Manuel Marulanda Vélez ya kafa kungiyar da ke yakin sunkuru a wani mataki na nemarwa talakawan wani yanki na kasar 'yanci. Su kan yi amfani da satar mutane da neman kudin fansa da kuma sayar da miyagun kwayoyi, suna takurawa mutanen da ke karkashin yankin da suke da iko da shi. cikin shekareu 50 din nan da suka gabata, ana kiyasin cewa sun kashe kusan mutane 200.000."

Kwalambiya dai kasashe da ta samu 'yancin kai tun gabanin yakin duniya na biyu. Bayan samun 'yancin kan sai aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan siyasar, ta yadda wasu ke neman a kare 'yan cin talakawa wasu kuma suka kasance 'yan jari hujja. Wannan shi ne asalin abin da ya haifar da yakin na kasar Kwalambiya. To tsakanin 'yan gurguzu da 'yan jari hujja sai aka samu kashe-kashe da rikici biyo bayan kashe guda daga cikin jagororin 'yan gurguzun, daga shekara ta 1948 zuwa 1958. A shekara ta 1960 an samu tsagaitaa wuta bayan dan dai-daito da aka samu, sai dai 'yan gwagwarmayar ba su yi na'am da yadda gwamnatin ta ce za ta yi rabon albarkatun kasa ba. hakan ne ya sanya suka kafa kungiyar FARC karkashin jagorancin Manuel Marulanda Vélez.

Bild-Kombi Farc-Rebellen

A baya cikin shekara ta 2011, shugaban kasar Kwalambiya Juan Manuel Santos ya bukaci da cewa a zauna kan teburin sulhu domin kuwa zubar da jinin ya isa. A cewarsa rikicin ya hana kasar ci-gaba baya ga bata mata suna a idanun duniya, suma a wannan lokacin kuwa a nasu bangaren 'yan tawayen FARC din sai suka amince domin kuwa tamkar yakin ya ishe su ne. A shekara ta 2014 sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta yadda za a kada kuri'ar raba gardama domin amincewa da wannan sulhu a wannan shekara ta 2016 da muke ciki.

To a ranar biyu ga wannan wata na Oktoba da muke ciki ne dai al'ummar ksar ta Kwalambiya suka kada kuri'ar raba gardamar, sai dai ba wani tasiri da ta yi. Wakilinmu na Bauchi Ado Abdullahi Hazzad ya tattauna da Sama'ila LIman Gamba, malami a kwalejin kimiya da fasaha ta Tatari Ali da ke Bauchi, wanda kuma ya yi karin haske kan wannan kuri'a ta raba gardama da al'ummar Kwalambiya suka kada.

Sama'ila:

"An kada kuri'ar raba gardama, sai dai wadanda suka kada kuri'ar basu wuce kaso 50 cikin 100 na adadin al'ummar kasar ba. A jimillance, wadanda ba su fito sun kada kuri'arsu ba kuwa sun kusa kaso 68 cikin 100.  Kwalambiya na da yawan al'umma kusan miliyan 45. Abin da suke so shi ne kawai a ci gaba da bude wuta a kan 'yan tawayen, a wajensu ba zai yi wu ba ace mutanen da suka kashe 'yan kasar masu yawan gaske ace kawai na kyale su ba. To a yanzu dai ana iya cewa an koma gidan jiya a wannan rikici na kasar Kwalambiya."

To sai dai rashin amincewa da sulhu da 'yan tawayen na FARC da al'ummar kasar ta KWalambiya suka yi, bai hana Shugaba Juan Manuel Santos  samun nasarar laashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta bana ba, wanda ya samu nasarar lashe wannan kyauta sakamakon yunkurinsa na kawo karshen yakin kasar ta hanyar kokarin ganin an yi sulhu tsakanin gwamnati da mayakan na FARC.