Tarihin taron Davos | Amsoshin takardunku | DW | 25.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin taron Davos

Tarihin taron shekara-shekara na birnin Davos ya samo asuli tun shekara 1971

default

Taron Davos game da tattalin arzikin duniya


Tarihin asulin taron Davos.

Birnin Davos dai, ya na cikin ƙasar Swezland,bisa tsauni mai tsawo, ya na ma ɗaya daga cikin birane da suka fi kasancewa kan tsaunuka mafi tsawo a duk faɗin  nahiyar Turai.

Idan muka dawo kanasulin taron Davos kuwa an ƙirƙiro shi tun shekarar 1971, wato kimanin shekaru 31 kena nda suka shuɗe.Wani Professa ne na jami´a mai suna Klaus M.Schwab ya ƙirƙiro wannan husa´a ta haɗa kan tebri guda, a ko wace shekara shugabanin kamfanoni da masana´antu, shugabanin ƙasashe masu tasowa da masu ƙarfin tattalin arziki, shugabanin addinai,masana, ´yan jarida da shugabanin ƙungiyoyi dabamdabam , domin tattatana batutuwa dabam-dabam da suka shafi rayuwar bani adama ta yau da kullum alal misali tashe -tashen hankula dake wakana  a duniya,ɗumamar yanayi, talauci da ya mamaye wasu ƙasashe a yayin da wasu ke rayuwa cikin wadata.A na shirya taron a ƙarshen watan Janairu na kowace shekara.Malaharta wannan taro na share kwanaki biyar suna masanyar ra´ayoyi a cikin komitoci dabam dabam.

To amma a tsawan shekaru 31 da aka ƙirƙiro taron Davos wace irin rawa ce ya taka ta fannin inganta rayuwar jama´a ?

A ɗaya wajen ana iya cewar ya zuwa yanzu wannan taro, bai tsinana komai ba, ta fanin burin da  wanda ƙirƙiro shi ya shata, domin duk da cewa an shirya shi har akalla so 40 amma har yanzu talaka na cikin talaucinsa,ana cigaba da ma´amila kashin dankali tsakanin manya da ƙananan ƙasashe duniya, kuma babu alamun al´amuran zasu cenzewa, wannan shine ma dalilin da ya sa wasu gungun Ƙungiyoyin masu radin inganta rayuwa suka kafa wata Ƙungiyar haɗin gwiwa, da zumar ƙalubalantar taron Davos.

A duk lokacin da ake gudanar da wannan taro, suma sai su kiri nasu taro, wanda sukewa take da "taron talakawa".Wato su a nasu nufi sun ɗauki taron Davos tamkar dai wani taro na masu hanu da shuni wanda kuma ba zai amfani talaka ba.

To saidai ta wani ɓangaren kuma, taron Davos ya na da amfani domin ko ba komai, a haɗu a gaisa, kuma  a tattana batutuwa dabam dabam.Sannan taron ya ɓullo da wata husa´a ta ƙarfafa gwiwa ga matasan dake ɗauke da burin girka kamfanoni da masan´antu, da kuma ƙasashe masu tasowa da suka yi hoɓa sarma ta fannin bunƙasa.

Sai kuma yunƙurin yaki da cin hanci da karbar rashawa da taron keyi.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Ahmed Tijani Lawal