Tarihin shugaban majalisar Jamhuriyar Nijer | Amsoshin takardunku | DW | 26.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin shugaban majalisar Jamhuriyar Nijer

Tarihin Ousseini Tinni shugaban majalisar dokoki ta Jamhuriyar Nijer wanda ya dauki madafun iko bayan kaddamar da majalisar.

Ousseini Tinni ya kasance dan jam'iyyar PNDS Tarayyar mai mulki kuma wanda ya zama shugaban majalisar dokoki bayan zaben da ya sake kawo Shugaba Mahamadou Issoufou a karo na biyu na wa'adin mulki.

An haifi Ousseini Tinni a watan Disamba na shekarar 1954, inda yake da kimanin shekaru 62 a haihuwa. A watan Maris na shekara ta 2016 ya zama shugaban majalisar dokokin bayan 'yan majalisa 118 sun kada kuri'a, yayin da 53 na bangaren 'yan adawa suka kaurace zaman majalisar. Majalisar dokoki ta kunshi mambobi 171.