1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin shugaba Mubarak

Kafin zama shugaban ƙasa, shine mataimakin shugaba Sadat

default

Shugaban Masar Hosni Mubarak

An haifi shugaba Hosni Mubarak ne a ranar 4 ga watan mayun 1928 a garin Kafr-ElMeselha dake ƙasar ta Masar. Bayan kanmala karatun sakandare ya shiga makarantar horas da hafsoshin jiragen sama, inda ya samu Digiri akan kimiyyar Sojojin ƙasa a 1949.

A ranar 2 ga watan Fabairun shekarar 1949 Mubarak ya bar makarantar Sojin ƙasa inda ya koma makarantar horas da sojojin majaƙan sama,inda kuma ya zama hafsan sojin sama mai muƙamin Pilot Officer a ranar 13 ga watan Maris ta shekarar 1950, tare kuma da samun wata Digirin a kimiyyan mayaƙan sama.

A matsayin sa na hafsan sojin sama Mubarak ya riƙe muƙamai daban-daban. Kafin a shekarar 1959 inda ya tafi makarantar koyar da mayaƙan sama dake birnin Moscow da Bishkek da yanzu ke ƙasar Kirgistan domin koyon dabarun yaƙin sojojin sama.

Jiragen da Mubarak ya ƙware wajen sarrafa su a wancan lokaci sun haɗa da Tupolev Tu-16. Bayan komowar sa gida a shekarar 1964 ya zama kwamandan makarantar horas da mayaƙan sama na Masar a sansanonin daban-daban dake faɗin ƙasar.

A shekarar 1967 Mubarak ya zama Babban kwamandan dakarun sojin saman ƙasar Masar, kafin kuma daga bisani ya zama Babban hafsan haɗin guiwan Sojin ƙasar baki ɗaya kuma mataimakin ministan tsaro. An yiwa Mubarak ƙarin girma zuwa Air marshal bisa gudumawar daya taka lokacin yaƙin Yom Kippur.

Bayan kisan gillar da masu kishin addini sukayi wa shugaban Masar na wanacn lokaci Anwar sadat a shekarar 1981, Hosni Mubarak ya zama shugaban ƙasar Masar kuma jagoran jam'iyar National Democratic Party. Yanzu haka dai Hosni Mubarak shine shugaba mafi daɗewa ne akan karagar mulki, inda yanzu yake shekaru 28 akan mulki.

Hosni Mubarak yana da aure, kuma sunar matar sa Suzanne Mubarak, suna da 'ya'ya biyu maza: Alaa da Gamal.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu