Tarihin Sepp Blatter shugaban FIFA
September 9, 2015Talla
An haifi Sepp Blatter shugaban hukumar FIFA ranar 10 ga watan Maris 1936 a kasar Switzerland inda yake da shekaru 79 da haihuwa. Ya fara shugabancin hukumar ta FIFA tun daga watan Yuni shekarar 1998. Ya yi karatu a kasar ta Switzerland zuwa matakin digiri a fannin kasuwanci da tattalin arziki.
Tun shekarar 1975 Blatter yake aiki da hukumar FIFA, inda ya rike mukamai daban-daban, kuma bayan sake lashe zaben shekara ta 2015, Blatter ya bayyana ajiye aiki domin bayar da dama a sake zaben sabon shugaban hukumar ta FIFA sakamakon rudanin cin hanci da rashawa da suka mamaye hukumar.
A bangaren iyali Sepp Blatter na da mata wadda suka rabu kuma ya sake aure hau sau uku, sannan ya na da 'ya daya.