1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Samuel Doe na Liberia

November 11, 2010

Tsohon shugaban Lberia Samuel Doe ya jogorancin ƙasarsa ƙarƙashin mulkin soja da kuma na farar hula.

https://p.dw.com/p/Q63u
Hoto: DW

Samel Kanyon Doe an haife fe shi ranar shida ga watan Mayu na shekara 1951 a wani gari mai suna Tuzon dake gabacin ƙasar Liberiya. A wannan ƙauye ya fara makarantar Firamari har zuwa 1967 inda ya ci jarabawar shiga Sekandare. Ya yi karatu a makarantar Sakadanri ta Zwedru amma tafiya ba ta yi nisa ba a ka kore shi daga wannan makaranta.Shekarunsa biyu rak a ciki.Daga nan ne sai aka ɗauke shi a aikin sojasoja.Rahotani sun ce ya nuna ƙwazo matuka a cikin aikin soja.

A shekara 1975 ya samu matsayin Sergent.Ya samu horo na musamman daga sojoji Amurika a shekara 1979. Kuma a wannan shekara ce ya kifar da mulkin shugaban ƙasa William Tolbert, ranar 12 ga watan Afrilu na shekara 1980, a yayin da ƙasar Liberiya ta fada cikin wani mummunan yanayi na tsadar rayuwa. Da juyin mulkin yayi nasara, sai ya naɗa kansa a matsayin Janar. Daga 1980 har zuwa 1985 ya shimfiɗa mulkin soja na kama karya, amma duk fa haka a tsukin wannan shekaru biyar Liberiya ta kasance ƙasar Afirka da ta fi samun tallafi daga Amurika.

A shekara 1985 Samuel Doe ya fara shimfada demokraɗiya inda aka zaɓe shi shugaban. To sai dai jam'iyun adawa sun ce an tafka maguɗi a wannan zaɓe.Daga nan ƙasar Liberiya ta sake faɗawa cikin wani sabon rikici siyasa.So da dama an sha yunƙurin kifar da shugaba Doe daga mukaminsa ba tare da cimma nasara ba. Sannu a hankali Amurika ta fara janye goyan bayanta daga Samuel Doe, da aka samu wasu ɓullar wasu ƙungiyoyin tawaye kamar na Independant Front da Prince Johnson ya jagoranta sai kuma NPLF na Charles Taylor.

Wannan ƙungiyoyi biyu sun haɗa kai domin ƙalubalantar Samuel Doe, sun yi nasarar cafke shi ranar tara ga watan Satumba na shekara 1990, inda su ka zi gudunwa gunduwa da shi. Wanda su ka kalli talabijin a daidai wannan lokaci, sun ga yadda 'yan tawayen su ka yi ta jan gawarsa bisa titi suka yanke masa kunnuwa da sauran sassan jikkinsa abin babu kyan gani.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu