1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tarihin NATO

Bikin cikwan shekaru 60 da girka Ƙungiyar tsaro ta NATO

default

NATO ta cika shekaru 60


A yau shirin duniya mai yayi za shi waiwaye adon tafiya a game girka wannan ƙungiya wadda shugabanin ƙasashe ko na gwamnatoci membobinta, suka ƙaddamar da bikin cikwan shekarunta 60 daidai ,a garuruwa ukku, dake kan iyakar Jamus da France.Zamu ji burin da NATO ke ɗauke da shi, da kuma ƙalubalen dake a gabanta,sannan muga yadda ƙungiyar ta faɗaɗa har zuwa ƙasashe 28 a yanzu.

Daga shekara ta 1939 zuwa 1945,jama´a tayi fama cikin uƙubar yaƙin duniya na biyu, wanda yayi kaca-kaca da ƙasashe da dama.

A wani mataki na riga kafi ga abkuwar irin wannan masifa,shugabanin ƙasashe da na gwamnatoci daga Amurika da ƙasashe Turai su 12 su yanke shawara girka ƙungiyar tsaro ta NATO a birnin Washington na Amurika:

Albarkacin bikin ƙaddamarwar shugaban Amurika Henri Trumann yayi jawabi:Ya ku shugabanin ƙasashe da al´umomin duniya!!! ina farin cikin bayyana maku girka Ƙungiyar NATO, wadda ke matsayin garkuwa, da kuma tubalin gina zaman lafiya mai ɗorewa a duniya.

A lokacin girka ta ƙungiyar NATO ta ƙunshi ƙasashe 12 wanda suka haɗa da Amurika, Belgium, Kanada, Danmark, Fransa, Britaniya Island, Italie, Luxemburg, Nowe, Holland, da Portugal.

Ƙudduri mai lamba biyar ke matsayin ƙashin bayan wannan ƙungiya, ya tanadi cewar, kai yaƙi ga ƙasa ɗaya memba a cikin NATO tamkar yaƙar sauran ƙasashen ne mebobinta.

Ernst Bevin shine ministan harakokinwajen Engila alokacinda aka girka kungiyar tsaro ta NATO a fira da yai da ´yan jarida jim kaɗan bayan taro,ya bayyana burin da NATO ta saga:

Minenev ya sa muka girka wannan ƙungiya? babbar amsa itace: tabbatar da zaman lafiya ta hanyar gama ƙarfi tsakanin ƙasashe.

Tsakanin yaƙe -yaƙe dake ɗaiɗaita ƙasashe ɗaya bayan ɗaya, mun fi buƙatar haɗin kai don wanzuwar zaman lafiya

A fakaice, girka wannan Ƙungiya na matsayin hannunka mai sanda ga Rasha da ma Jamus da tayi sanadiyar ɓarkewar yaƙin duniya na biyu.

A watan Oktober na shekara ta 1954 Kungiyar NATO ta gayyaci Jamus ta zama memba, domin mika tata gudunmuwa a wannan saban yunƙuri, na wanzar da zaman lafiya a duniya.

Shugaban gwamnatin Jamus na wacen lokaci Konrad Adenauer ba da wata wata aba ya karɓi goran gayyatta a cikin wani jawabi da ya gabatar:

Ra´ayin gwamnatin Jamus shine cewar, Tarayya Jamus tayi lale marhabin da tayin shiga wannan ƙungiya da ƙasashe membobinta suka yi mana.A shirye muke mu bada haɗin kai ,muddun hakan zai tasiri, ta fannin samar da zaman kwanciyar hankali, da kuma kyauttata rayuwar jama´armu.

A hukunce, ranar 9 ga watan Mayu na shekara ta 1955, shugaban gwamnatin Jamus Konrad Adenauer, ya rattaba hannu akan yarjejeniyar shigar da Jamus a ƙungiyar NATO, to saidai tafiya bata yi nisa ba,aka samun saɓani a harakokin tafiyar da Ƙungiyar, inda wasu ƙasashe suka zargi Amurika da zama uwa makarɓiya, a game da haka shugaban ƙasar France Charles Degaulle a watan Maris na shekara ta 1966, ya yanke shawara fidda ƙasarsa daga komitin ƙolin, ya bada hujjojin tare da cewa:

Wannan mataki mun ɗauke shine badan komai ba, face mu tabbatar da cikkaken´yancin ƙasarmu.

Tun ƙarshen yaƙin duniya na biyu, ƙasar Jamus ta tsinkin kanta a cikin halin watanda, tsakanin Rasha da sauran ƙasashen da suka ci yaƙi, saidai katangar Berlin da ya raba Jamus ɓangare biyu, ta rushe a shekara ta 1989.

Ba jamusawa kaɗai ba, suka nuna farin cikin rushewar katangar Berlin ,har ma da Ƙungiyar tsaro ta NATO, wacce ta samu damar faɗaɗa, zuwa ƙasashen yankin gabacin Turai, inda Rasha ke da babban angizo. Hukumar zartaswa ta NATO ta yanke shawara fara karɓar wannan ƙasashe a taron ƙolin da ta shirya, a birnin Madrid na ƙasar Spain, kamar yadda Sakatare Janar na NATO a lokacin wato Havier Solana yayi bayyani:

A yau shugabanin ƙasashe da na gwamnatoci, sun amince su shiga tattanawa da Jamhuriya Cek, Hongrie da Poland, domin karɓar su, nan da ´yan shekaru masu zuwa, a matsayin membobi a cikin NATO.

Bayan wannan ƙasashe ukku sannu a hankali ,NATO ta cigaba da karɓar sabin ƙasashen yankin gabacin Turai,musamman bayan watsewar Tarayya Soviet abunda ya ƙara hadasa tsamin danganta tsakanin hukumomin Mosko da NATO.

Albaniya da Kroatiya sune cikkamakon ƙasashe na 28, da suka samu shiga NATO, albarkacin taron cikwan shekaru 60 ga girkuwar wannan Ƙungiya.

A cikin tarihinta, NATO ta aika sojoji a yankuna da dama da suka yi fama da tashe tashen hankula.Wasu daga tawagogin NATO mafi masu mahimmanci sun haɗa da wanda ta tura Kosovo, da Aganistan, bayan hare-haren da suka rutsa da Amurika a watan satumba na shekara ta 2001.

A lokacin mulkin shugaba Georges Bush,Amurika da abokan ƙawancenta na NATO, sun ƙaddamar da wani gagaramin shiri na yaƙi da ta´danci a ƙasar Afganistan, to saidai an samu rabuwar kanu tsakanin ƙasashen NATO a game da siyasar gwamnatin tsofan shugaban Amurika ta yaƙi da ta´adanci, abunda ya hadasa koma baya a harakokin gudanarwa na NATO.

Saidai Ƙungiyar, tayi amfani da taron ƙolin da ta shirya a kan iyar France da Jamus, daga 3 zuwa 4 ga watan Afrul na shekara ta 2009, domin ɗinke ɓaraka, da kuma shirya sabuwar tafiya.

Shugaban ƙasar Amurika Barack Obama, da ya halarci wannan taro a karon farko,ya bayyana aniyar ƙasarsa ta cimma burin da NATO ta sa gaba.

Bayan yini biyu na mahaurorin shugabanin, sun cimma matsaya guda akan wasu batutuwa masu mahimmanci, Barack Obama ya bayyana wasu daga cikinsu:

Mun samu babban cigaba.Yanzu Albaniya da Croatiya sun zama membobin a cikin NATO.Sannan Fransa ta sake maye gurbinta a komitin koli , kazalika mun ɓullo da wasu ƙarin matakai wanda zasu bamu damar fuskantar ƙalubalen zamani.

Wannan ƙalubale da Barack Obama ke magana akai, ya haɗa da kakkaɓe al´amuran ta´adanci, mussamman a ƙasar Afganistan, inda ƙasashen Turai, suka karɓi kiran shugaban Amurika, na ƙara yawan dakaru a cikin rundunar NATO ,domin fuskantar turjiyar ´yan taliban da Alqa´ida.

A ɗaya hannun shugabanin ƙasashen NATO, sun yanke shawara inganta ma´mila da ƙasar Rasha, da kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a sabuwar ƙasar Kosovo.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.

Edita: Abdullahi Tanko Bala