1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Musa Dankwairo

Abba BashirJuly 31, 2006

Bayani akan Marigayi Alh. Musa Dankwairo

https://p.dw.com/p/BvVL
Kayan Kidan Zamani
Kayan Kidan Zamani

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aiko mana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Muhammad Idris Waziri mazauni a garin Keffi da ke Jihar Nassarawan Tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya ke yi ; Don Allah ku ba ni tarihin Marigayi Alhaji Musa Dankwairo, a wace shekara aka haife shi, yau she ya soma waka kuma yayansa nawa?

Amsa : To mundai mika wannan fatawa ga wakilin mu na Jihar Katsinana a tarayyar Najeriya, wato Salisu El Mansur, inda shi kuma ya yi mana hira da Farfesa A. M. Bunza na Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto da kuma babban Dan marigayi Musa Dankwairo, wato Alhaji Garba Musa Dankwairo. Amma ya fara ne da zantawa da Farfesa A. M. Bunza ga kuma yadda hirar tasu ta kasance;

El Mansur:Farfesa, Ko zaka ga ya mana takaitaccen bayani game da Marigayi Alhaji Musa Dankwairo?

Bunza: To shi dai Marigayi Musa Dankwairo kamar yadda muka sani mawakin fada ne ga gado.

El Mansur: Farfesa ko a wacce shekara aka haifi Musa Dankwairo?

Bunza: A takaice an haifi Alh. Musa Dankwairo a shekarar 1907 a garin Bakura wanda tsakanin Bakura da Sokoto, akwai tazarar kilomita 105. Sunan Mahaifinsa usman Dankwanda. Shi Usman Dankwanda ya rayu a Kaya ne kuma yana yiwa sarkin Kayan Maradun Waka, Mahaifin Dankwairo da kakansa duk makadan sarkin kayan Maradunne. Ya tashi ya tarar da kakansa da Mahaifinsa suna waka tare, amma ya fi rayuwa da mahaifinsa rayuwa ta hakika. Kuma tun yana Dan shekara 6 zuwa 7 mahaifinsa ya ke zuwa da shi a cikin tsangaya ta waka, sabanin irin su Dandada Aliyu mai-taushi da Na-rambada da gaba daya basa zuwa da Yayansu, su sun dauki waka kaddarace ta shigar da su shi ya sa basa son Yayansu su gaje su.

El Mansur: To mai ya faru bayan rasuwar Mahaifin Alhaji Musa Dankwairo?

Bunza: To bayan rasuwar mahaifinsa sai kungiyar waka ta koma hannun Aliyu Kurna wato wan Dankwairo kenan, shi kuma Musa Dankwairo sai aka zabe shi ya zama mataimakin Aliyu Kurna, idan Aliyu Kurna bayanan sai Dankwairo ya zama shine shugaban tawaga.

El Mansur: farfesa to yaushe Alhaji Musa Dankwairo ya sami wannan Lakabin suna nasa wato(Dankwairo) ?

Bunza : Ya samu wannan lakabi na Dankwairo tun lokacin da Mahaifinsa na da Rai.Mahaifinsa ya na da wani Yaro da ake kira Dankwairo, saboda yaron zakin murya gare shi da kuma kwarewa wajen karbin waka, to sai Musa ya rinka kwaikwayonsa tare da kwaikwayon muryarsa , to da aka ga musan ya kware kamar shi Dankwairon na asali, sai shima ake kiransa da wannan lakabi na Dankwairo.

El Mansur: Kana ganin Yayan Marigayi Musa Dankwairo, zasu iya daurewa su ci gaba da rungumar wannan waka da daraja kamar yadda mahaifinsu ya yi ?

Bunza : To da yake shima Dankwairo ya tarar da mahaifinsa ne yana yi kuma bayan rasuwarsa ya ci gaba to suma Yayannasa ba bu shakka zasu iya yin iyakacin kokarinsu, amma baza mu iya cewa zasu dauki matsayin sosai-sosai ba saboda kusan Sarautun da ake yi wa wakar sun dan yi rauni yanzu, Tunda yanzu harkar mulki ta koma ga hannun Yan-siyasa da Sojoji Masu Mulkin kama karya in sun hau mulki.

El Mansur: Mai ya sa Dankwairo ya zauna a gindin Marigayi Sardaunan Sokoto?

Bunza: To Musa Dankwairo ya yi wa Sardauna wakoki guda 17 amma mu a wajenmu 12 muka tantance muka san da zamansu kuma muka tabbatardasu. Dalilin Saduwar sa da Sardauna kuwa a fagen siyasar NPC ne su ka hadu. Saboda Sardauna ga shi Dansiyasa kuma Dan-sarauta, ka ga yana bukatar wani mawakin Sarauta da zai zauna tare da shi, Wannan shine asalin saduwarsa da Dankwairo, kuma wakar da Dankwairo ya fara yi wa Sardauna ita ce Wakar (Mai dubun nasara garnakaki Sardauna).

El Mansur: Alhaji Garba, Kana daga cikin manyan Yayan Marigayi Musa Dankwairo,to ku nawa ne ya mutu ya bari?

Garba: To mata 7, maza 7 Mahaifinmu ya bari lokacin da ya rasu wato mu goma-sha-hudu kenan. Kuma a lokacin da ya rasu ya na da Jikoki Dari da Hudu 104, kuma ba a nan muka tsaya ba, domin kuwa bayan rasuwarsa munci gaba da haihuwa.